Daga UMAR GARBA a Katsina
Rundunar ‘yan sanda ta Jihar Katsina ta bayyana cewar ta samu nasarar kashe wasu manyan shugabannin ‘yan bindiga uku da su ka addabi al’umar jihar.
Daga cikin waɗanda aka kashe akwai ƙasurgumin ɗan bindiga Bala wuta wanda ya addabi ƙaramar hukumar Jibiya, sauran su ne Dogo na Sahura da kuma Hassan Bukuru.
Bayanin haka na ƙunshe cikin wata sanarwa da Kakakin rundunar, ASP Abubakar Aliyu ya fitar ranar Laraba a Katsina.
Ya ce, arangamar ta faru ranar 25 ga watan Nuwamba,2023 da misalin ƙarfe 10:30 na safe lokacin da su ke gudanar da sintirin haɗin gwaiwa tsakaninsu da ‘yan banga a ƙauyen kwarare dake ƙaramar hukumar Jibiya.
“Wasu da muke zargi ‘yan bindiga ne sun buɗe mana wuta lokacin da mu ke sintiri, nan da nan jami’an tsaronmu suka mayar da martani, hakan ya tilasta wa ‘yan ta’addar fasa muguwar aniyarsu inda su ka tsere cikin daji.
“A yayin da mu ke bincike a wurin da lamarin ya faru mun gano gawarwakin ‘yan ta’addar da aka kashe da kuma babur ɗinsu,” inji shi
ASP Aliyu ya ƙara da cewa daga baya an gane cewar waɗanda aka kashe sune Bala wuta, ɗan ta’addar da ake zargi shugaban ɓarayin daji ne a ƙaramar hukumar Jibiya da kewayenta.
A cewar sa rundunar na ci gaba da ƙoƙarin kamo waɗanda suka gudu.
Kakakin ya kuma bayyana cewar kwamishinan ‘yan sanda na jihar Aliyu Abubakar Musa, ya yaba wa jaruntar ‘yan sandan ya kuma buƙace su da su ci gaba da jajircewa.
Kwamishinan ya kuma roƙi al’umar jihar akan su ci gaba da bawa rundunar muhimman bayanan aikace aikacen ‘yan bindigar, a cewarsa hakan zai taimaka wa jami’an tsaro ɗaukar matakin da ya kamata kan lokaci don kawo ƙarshen aika aikar ‘yan bindiga.
