Yadda ma’aurata za su cigaba da raya soyayyarsu bayan aure (1)

Spread the love

Tare da AMINA YUSUF ALI

Barkanmu da sake haɗuwa a wannan jaridar taku mai farin jini ta Blueprint Manhaja. Yau za mu tattatuna a game da abubuwan da maaurata za su yi don cigaba da raya soyayyarsu ko da bayan an yi aure. Abinda uka sani ne, kuma ba ɓoyayyen abu ba ne soyayya takan mutu murus bayan aure.

Akwai dalilai da yawa da sukan sa hakan ta faru. Wannan ya sa a wannna mako muke tafe da waraka a kan wannan laura da ta kan gallabi kusan kowanne aure. Shi ne ni kuma na yi linqaya a kogin zamantakewa na tsamo muku wasu daga cikin hanyoyin da za su iya zama mafita a kan waɗancan matsaloli. Wato yadda za a raya soyayya ta ci gaba da bunƙasa ko da bayan an shafa fatiha har ma bayan zaman ya yi zama. Bismillah, a sha karatu lafiya.

  1. Soyayya don Allah: Mafita ta farko da za ta haɓaka soyayya tsakanin ma’aurata ita ce so don Allah. So don Allah shi ne wanda nisa ko sauyawar halitta ko halayya ba sa canza shi. Son gaskiya shi ne wanda ake yinsa ba don komai ba. To ita soyayyar gaskiya tunda ba a ɗora ta bisa komai ba sai don Allah ba ta mutuwa. Tana kasancewa rayayya ko da bayan masu yinta sun bar Duniya.
  2. Girmamawa da mutunta juna: Mutunta mutum yana ɗaya daga cikin dalilan da suke sa soyayya ta havaka a zukata. Idan ma’aurata suna mutunta juna ta hanyar shawara da juna, tausasa kalamai, kiyaye ɓacin ran juna da sauransu. Rashin yaudarar mutum da yi masa ƙarya shi ma yana cikin mutuntawa. Wannan yana sa su ji a ransu ba kamar su. Kuma soyayyar wanda yake mutunta su ɗin ta ƙara yauƙaƙa a zukatansu.
  3. Gyara kai: Gyara kai kamar tsafta da kwalliya wasu hanyoyi na ta da komaɗa ne da suke ƙara sa zukata su qara dilmiyewa a soyayya. Haƙiƙa dukkan ‘yan Adam Allah ya halicce su da son tsafta da ƙyale-ƙyale. Ado da gyara yana janyo hankali matuqa. Don haka idan ma’aurata suna kwalliya da tsafta domin juna, mawuyacin abu ne a ce soyayyarsu ta mutu murus.
  4. Kyautatawa ga juna: Kautatawa juna shi ma wani jigo ne da yake tabbatar da soyayya ba ta gaza ba a tsakanin ma’aurata. Kyautatawa za ta iya zama ta hanyar yi wa juna kyauta ta ban mamaki, girmamawa, tausayawa, tallafawa wajen yin aikin gida ko raino. Ɗaukar mace a mota a kaita inda za ta, da sauran abubuwa da suka danganci hakan. Kamar yadda na faɗa a sama, kyautatawa ta fi dukkan sauran hanyoyin saurin isar da saƙon so da kuma ninka soyayya a kowanne lokaci.
  5. Kulawa da juna: Bayan kyautatawa, kulawa da juna ita ce kusan hanya ta biyu ma fi ƙarfi wajen ƙara zuba wa dashen so ruwa da taki. Don ƙara haɓaka tsiron ƙauna. Kula da juna ya hada da yi wa juna waya ko saqon tes a kai-a kai don nuna kulawa, tausayawa yayin da ɗaya ya shiga halin rashin lafiya ko damuwa. Ba wa aboki ko abokiyar zama qwarin gwiwa da taimako duk sanda bukatar hakan ta taso, Kula da buƙatun juna tare da biyan bukatun inda ba za su gagara ba, nuna wa juna soyayya ƙarara ba tare da kunya ko shayi ba, da sauransu. Waɗannan matakan suna ba da mamaki matuqa wajen haɓaka soyayyar ma’aurata. Har ma da sauran alaƙoƙi.
  6. Girmama magabatan juna da dangi: Girmama magabatan juna ma yana matuƙar tasiri wajen raya soyayya. Ma’aurata da dama sukan zauna da juna ko ba so in dai ana mutunta iyayensu sukan karanta su ma su dinga kyautata wa abokin zama.
  7. Haƙuri da yin uzuri: Yana daga abinda yake ƙara raya soyayya tsakanin ma’aurata. Ma’auratan da suke haƙuri da juna sun fi samun kwanciyar hankali. Kalmomin nan da iyaye kan faɗa wa ma’aurata cewa: a ji, a ƙi ji. A gani, a ƙi gani. Tana da matuƙar alaƙa da haƙuri. Wato mu sani abokin rayuwa ba ma’asumi ba ne. Ko da bai yi niyya ba wasu lokutan ana samunsa da kufcewa ya yi abinda bai kamata ba. Idan hakan ta faru sai a yi masa/mata uzuri. A tuno kyawawan abubuwanda ya yi ko ta yi a baya. Saboda rayuwa haka ta gada kowa yana son a yi masa uzuri kuma a yafe masa idan ya yi ba dai-dai ba. Idan ka yafe laifin wani yau, kai ma gobe sai a yafe maka. Masoyan da suke wa junansu uzuri kan kasance cikin rayuwa mai daɗi. Da fahimtar juna. Kuma soyayyarsu ba ta taɓa durƙushewa. Saboda haƙuri da juriya da uzuri su ne abincin soyayya waɗanda idan ta rasa su takan mace.

A nan za mu dakata. Sai wani makon idan mai dukka ya nufa za mu cigaba daga inda muka tsaya.

In godiya ga dukkan makaranta da abokan arziki da auka jajanta min da yi min ta’aziyyar rasuwar Mahaifina Sheikh Dakta Yusuf Ali Kano. Allah ya yi masa rahama, ku kuma Allah ya saka muku da alkhairi.

Za a same ni a kan lambar waya: 08024859793.

By Editor