‘Yan bindiga sun kashe ‘yan sanda biyu a Imo

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

Aƙalla mutum uku ciki har da ‘yan sanda biyu sun mutu sakamakon sabon harin da ‘yan bindiga suka kai a yankin Ƙaramar Hukumar Ahiazu Mbaise, Jihar Imo.

Rahotanni sun ce, harin ya auku ne a ranar Litinin, 27 ga Nuwamban 2023, inda ɓata-garin suka buɗe wa ‘yan sandan wuta wanda a nan take suka hallaka jami’ai biyu da wani mutum guda.

Majiyarmu ta ce harin ya auku ne a lokacin da sabon Kwamishin ‘Yan Sandan Jihar, Danjuma Aboki, ya kai ziyarar aiki a yankin Mbaise domin ƙara wa jami’ansu ƙwarin gwiwa.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, Henry Okoye, ya tabbatar wa jaridar Punch aukuwar lamarin.

Okoye ya ce tuni rundunar ta duƙufa da bincike domin gano waɗanda ke da hannu cikin aikata wannan ɗanyen aiki.

Jihar Imo na daga cikin jihohin da ‘yan bindiga ke hana jami’an tsaro sukuni a Nijeriya.

By Editor