*Sojoji sun kammala atisayen “Operation Mugun Bugu”
Daga BASHIR ISAH
Babban Hafsan Tsaro na Nijeriya, Janar Christopher Musa, ya yi kira da a ƙara tallafin da ake bai fannin tsaro musamman ɓangaren mayaƙan sama domin ci gaba da ƙarfafa musu game da yaƙi da matsalar tsaro.
Kiran na zuwa ne a lokacin da Rundunar Sojin Nijeriya ke kammala atisayen “Operation Mugun Bugu” na makonni wanda shi ne irinsa na biyu da ta shirya a 2023.
Yayin atisayen wanda ya gudana a garin Kontagora, Jihar Neja, dakarun sun yi gwajin makamai tare da ɗaukar sabbin dabarun aiki.
Da yake jawabi ta bakin wakilinsa Manjo Janar Jal Jimoh, Janar Musa ya jaddada muhimancin rundunar mayaƙan sama wajen yaƙi da matsalar tsaro.
Daga nan, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su haɗa kai sannan a riƙa taimaka wa sojoji da muhimman bayanan da za su taimaka wajen daƙile matsalar tsaro a sassan ƙasa.
Babban Hafsan ya ce atisayen ya gudana cikin nasara an kuma kammala shi ƙalau.
