Masu aikata laifi a Filato, Benuwai da Nasarawa su shiga taitayinsu, inji rundunar AIG da aka tura

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Sabon Mataimakin Sufeto Janar, AIG, mai kula da hedikwatar shiyya ta 4 da ke Makurdi, Mista Ebong Eyibio, ya yi gargaɗin cewa babu inda za a yi laifi a yankinsa.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da aka raba wa manema labarai a ranar Alhamis, mai xauke da sa hannun jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan shiyya ta 4, PPRO, ASP David Kaavanger, kuma aka miƙa wa Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya a Makurdi.

Mista Eyibio ya ce zai tabbatar da cewa masu aikata laifuka ba su da gurbi a jihohin Benue, Filato da Nasarawa da ke ƙarƙashinsa.

Ya kuma buƙaci haɗin kan al’umma wajen yaqi da miyagun laifuka a shiyyar.

Ya gargaɗi masu aikata laifuka a shiyyar da cewa babu inda ake aikata laifuka a ƙarƙashin kulawarsa, ya kuma ce dukkansu su juya baya su daina aikata laifuka ko kuma su fuskanci fushin doka.

A cewar sanarwar, Sufeto Kayode Egbetokun, ya naɗa AIG Ebong Eyibio a matsayin mataimakin babban sufeton ‘yan sanda da ke tuhuma.

By Editor