NUJ ta yi tir da cin zarafin ɗan jarida a Neja

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Cikin makon da ya gabata ne Kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro na jihar Neja, Manjo Janar Bello Mohammed Abdullahi (mai ritaya) ya ci zarafi, tare da tozarta wakilin gidan Radiyon Muryar Amirka na jihar Neja, Alhaji Mustapha Nasiru Batsari.

Da ya ke nuna takaicin sa game da wannan lamari, Shugaban Ƙungiyar ‘yan jarida ta qasa NUJ, reshen jihar Neja, Kwamared Abu Nmadu ya bayyana wannan abu a matsayin abin takaici.

Abu Nmadu ya ci gaba da cewa sun kaɗu matuƙa da jin faruwar wannan lamari, wanda ya ce ba za su tava lamuntar irin wannan ɗanyen aikin a kan mambobin su a jihar ba.

Haka shi ma, Shugaban Ƙungiyar wakilan kafafen yaɗa labarai ta ‘Correspondents Chapel’ na jihar, Kwamared Yakubu Mustapha Bina, cewa ya yi, duk da dai wannan irin ɗabi’a ita ce halayyar Kwamishinan, amma dai ƙungiyar ba za ta sake ɗaukar wannan cin zarafi ba.

Shugaban ya ce, bayan buƙatuwar da su ke da ita na wannan Kwamishina na ya fito fili ya nemi afwa, to, ba za su tava lamuntar wani cin zarafi ko barazana daga wani ma’aikacin gwamnati ba.

Daga nan sai Kwamared Mustapha Bina ya shawarci Gwamna Mohammed Umar Bago da ya lalubo wani ƙwararre, masani, wanda zai ɗinke wannan ɓaraka da aka samu.

Ita dai wannan badaqala ta faru ne a lokacin da wakilin na VOA ya dumfari Kwamishinan a gidan gwamnatin jihar domin jin ta ɓangaren gwamnati game da yadda za a kauce wa ramuwar gayya a wani rikici da ya afku na al’ummar Beji.

Wato, wani rikici ne ya afku tsakanin Fulani da Gwarawa a Beji da ke Ƙaramar Hukumar Bosso ta jihar Neja, wanda kuma ya yi sanadiyyar mutuwar mutum huɗu da jikkata wasu mutum tara.

Da ya ke bayyana yadda al’amarin ya afku, Alhaji Mustafa Nasiru Batsari ya yi nuni da cewa, ya kira Kwamishinan a waya a lokuta da dama, amma babu amsa, ya kuma je ofishin sa, bai same shi ba, kwatsam sai ya yi kicivis da shi a gidan gwamnatin jihar, inda ya tunkare shi ciki lumana, amma abin sai ya ga wannan cin mutuncin.

Ya ce, da taimakon Allah, da taimakon wasu jama’a ne suka cece shi daga hannun Kwamishinan, wanda kuma ya yi masa barazanar sai ya yi maganin sa, tare da ƙoƙarin ƙwace masa na’urar ɗaukar magana.

Daga nan Alhaji Batsari ya nuna matuƙar damuwar sa, musamman ganin yadda wannan cin zarafi ya fito ne daga mutumin da ya yi ritaya a matsayin babban muqami na soja, sannan ya ke riƙe da muƙamin kula da tsaron rayuka da dukiyar jama’a.

“Wannan ya sa na ke da shakkun cancantar sa a riƙe wani muƙami na gwamnati,” inji Batsari.

By Editor