Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
A ranar Asabar ɗin makon da ya gabata ne Zauren Mata da aka fi sani da “Mata Annual Conference” suka gudanar da taronsu na shekara a jihar Kano.
Taron wanda ya samu halartar mata da kamfanoni daga ciki da wajen jihar Kano inda aka gudanar da jawabai na ƙarfafa gwiwar mata akan sana’o’i na dogaro da kai da kuma kyautata zamantakewa da mazajensu.
Da take jawabi akan maƙasudin taron ɗaya daga cikin jami’ar da suka shirya taron, Stephnie Obia wacce ‘yar ƙabilar Ibo ce haifaffiyar jihar Kano ta ce wannan shi ne taro karo na biyar na shekara da suke gudanarwa.
Ta ce lokacin da suka kafa zauren kamar da wasa ta yanar sadarwa ba su wuce su bakwai ba a 2018 sai aka bada shawarar a fara gayyato mata abin ban mamaki sun soma da gayyatar mata 300 amma 700 suka halarta.
Stephnie Obia ta ce sai a shekara ta 2019 suka sake taro na biyu shi ma aka samu gagarumar halarta har suka yi taro na uku da na huɗu amma a lokacin annobar Korona ne ba su samu sun yi ba sai wannan karo da shine na biyar.
Ta ce da taron na Kano ne amma yanzu ya wuce ya zama da Arewa da ƙasa baki ɗaya don an samu waɗanda suke halarta daga Legas.
Sannan ta ce taron ba ana nunawa mata su kangarewa mazajensu ba ne, a’a ana nuna musu cewa yadda za su tsaya da ƙafafunsu kan sana’o’i don su riqa tallafan juna cikin biyayya da mutuntawa.
Ta ce duba da cewa yanzu an wuce zamanin da za a zuba wa mazaje ido duba da halin da ake ciki shine suke ƙarfafarsu akan yin sana’o’i na dogaro da kai ba tare da an matsawa miji da kawo-kawo ba.
Stephnie Obia ta ce yanzu haka suna da mambobi a zauren da suka 2000 daga sassan ƙasar nan.
A yayin taron an karrama wasu mata da suka yi fice a ayyukan gwamnati da sana’o’i na dogaro da kai har da masu kamfanoni.
