2023 AFCON: Dole ne Super Eagles su saka tunanin cin nasara – Aghahowa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Tsohon ɗan wasan Nijeriya, Julius Aghahowa ya buƙaci Super Eagles da su bunƙasa tunanin samun nasara a gasar kofin Afrika na 2023.

A rukunin A da Cote d’Ivoire, Equatorial Guinea da Guinea-Bissau, zakarun na AFCON sau uku za su sake lashe gasar karo na huɗu.

Super Eagles za ta buxe gasar ta ne a AFCON 2023 da Equatorial Guinea a filin wasa na Alhassan Quattara, Ebimpe ranar 14 ga watan Janairu.

Sai dai a wata hira da Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya (NAN), Aghahowa ya bayyana cewa dole ne ‘yan wasan su nuna jajircewa da juriya idan suna son yin tasiri mai kyau a gasar.

“‘Yan wasan suna cikin Turai wanda ya fi sauƙi saboda kowa yana wasa iri ɗaya, amma zuwa Afirka don buga wasa da fafatawa a manyan gasa kamar wasannin neman gurbin shiga gasar kofin duniya ko AFCON, ba za mu sami sauqi ba,” Aghahowa ya gaya wa NAN.

“‘Yan wasan za su iya yin hakan, kuma na yi yarda da su, amma wannan sadaukarwa da juriya cewa wasan ya zama dole ne a yi nasara a cikin tunaninsu,” inji shi.