Amurka da Saudiyya sun gaza kawo ƙarshen rikicin Sudan

Spread the love

An gaza samar da cigaba a tattaunawar kawo ƙarshen rikicin Sudan da Saudiyya da Amurka suka kasance masu shiga tsakani, yayin da rashin jituwa tsakanin manyan hafsoshin sojin ƙasar biyu ta haifar da ƙalubale ga ayyukan jin ƙai a ƙasar.

Rashin cigaba a tattaunawar da ke faruwa a birnin Jedda, ya rushe fatan da mutum sama da miliyan shida da rabi a ciki da wajen ƙasar ke yi, abin da ya ƙara haifar da taɓarɓarewar tattalin arziki da kuma rikicin ƙabilanci a Darfur.

Yayin da rundunar sojin Sudan ɗin ta ce, ta ƙwace ikon babban birnin ƙasar, Khartoum, dakarun kai ɗaukin gaggawa na RSF kuma sun faɗaɗa ayyukan ne a yankuna Darfur da kuma Kordofan.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka, masu shiga tsakani a shirye suke a ci gaba da tattaunawar neman mafita.

A ranar Litinin ne, gwamnatin Amurka ta sanya takunkumi kan wasu manyan jami’an tsaro biyu da suka yi aiki ƙarƙashin tsohuwar gwamnatin Omar El-Bashir, sakamakon zarginsu da hannu wajen rura rikicin Sudan.

A ranar Asabar ɗin makon jiya ne, Janar Abdel Fattah al-Burhan ya shaidawa wani taron soji da aka gudanar cewa, wannan yaƙi ba zai ƙare ba, har sai gwamnati ta ƙwato dukkanin yankunan ƙasar da ke hannun ‘yan tawaye.

Yanzu haka dai, rundunar RSF ta sake buɗe kasuwanni da asibitoci tare da tura ‘yan sanda aiki a sassan Darfur.

By Editor