Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau
Dakarun rundunar haɗin guiwa ta arewa maso yammacin Najeriya Operation Hadarin Daji (OPHD) sun daƙile harin da ‘yan ta’adda suka kai kauyen Danjibga dake ƙaramar hukumar Tsafe tare da daƙile ɓarnar amfanin gona a ƙauyen Faru dake ƙaramar hukumar Maradun duk a jihar Zamfara inda suka samu nasarar Kashe wasu da dama a batakashin da suka yi.
Sojojin sun ce a yayin arangamar da ‘yan ta’addan sun samu nasarar hallaka guda uku daga cikin ‘yan ta’addan, an kuma ƙwato bindigogi kirar AK-47 guda 3, kwanson alburusai 3, da kuma babura biyu.
“A ranar 7 ga watan Disamba, 2023, dakarun haɗin gwiwa na Operation HADARIN DAJI (OPHD) sun daƙile wani harin ta’addanci da suka kai ƙauyen Danjibga dake ƙaramar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara, biyo bayan wata mummunar gobara da ta yi sanadin kashe biyu daga cikin ‘yan ta’addan yayin da wasu suka tsere da harbin bindiga.” .
Sojojin hakazalika sun ƙwato bindigu kirar AK47 guda 2 da kwanson alburusai 2 da babur daya (1) a yayin batakashin da ‘yan ta’addan.
A yayin arangamar a shiyyar ƙaramar hukumar ta Marathon an kashe ɗan ta’adda daya (1) yayin da aka samu bindiga ƙirar AK 47 guda 1, alburusai da babur daya (1) yayin da aka lalata babur din nan take.
