Gwamnan Katsina ya bada umarnin dakatar da malami bisa zargin lalata da ɗalibarsa

Daga UMAR GARBA a Katsina

Gwamnan jihar Katsina Umar Dikko Raɗɗa, ya bayar da umarnin dakatar da wani shugaban makarantar sakandare ta gwamnati da ke garin Ɗantankari a ƙaramar hukumar Ɗandume, bisa zarginsa da neman ɗalibarsa da lalata.

Bayanin haka na ƙunshe cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai na ofishin sakataren gwamnatin jihar Abdullahi Aliyu ‘Yar’adua ya saka wa hannu.

A cewar sanarwar “Mai girma Gwamna ya karvi rahoton dake nuni da cewa ana zargin wani Lawal Ibrahim akan cin zarafin wata ɗaliba ta hanyar nemanta da lalata wanda shugaban makarantar sakandaren Ɗantankari ne dake ƙaramar hukumar Ɗandume.

“Saboda haka ne gwamnan ya bawa kwamishinan ma’aikatar ilimin firamare da sakandare umarni akan a dakatar da Lawal Ibrahim nan take, don gudanar da bincike tare da ɗaukar matakin da ya dace game da lamarin.

Kazalika, ana zargin DPO na ‘ƙaramar hukumar ta Ɗandume akan karɓar rashawa don ɓoye maganar.

Don haka ne gwamna Raɗɗa ya bawa kwamishinan ‘yan sanda na jihar umarni, akan a binciki DPO na ‘ƙaramar hukumar game da zargin rufa rufa dangane da lamarin.