Kashi 70 na ma’aikatan kamfanin Mamuda ‘yan Kano ne – Gaddafi

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Gaddafi Isyaku Hassan, jami’in cinikayya na kamfanin Mamuda, ya ce suna bada gudunmuwa ga mata domin ƙara musu ƙwarin gwiwa wajen sana’ar dogaro da kai, tarbiyya a zamantakewarsu na rayuwar aure a tarukansu daban-daban.

Ya bayyana hakan ne ga manema labarai a wani taro da wasu mata suka gudanar da kamfanin ya bajekolin kayyakinsa da makarantu don qara musu ƙwarin gwiwa.

Jami’in ya ce irin gudummuwar da suke bayarwa bai tsaya ga cigaban mata kaɗai ba har da ɓangaren ilimi har sai da ma’aikatar ilimi ta jihar Kano ta karramasu bisa irin jajircewa da  taimako da suke bai wa ilimi na zamani da na addini.

Ya ce baya ga haka suna taimakawa ƙungiyoyin ‘yan kasuwa a kasuwanni da tallafi da kuma gina rijiyoyin burtsatse a masallatai da muhimman wurare da suka haɗa da tsangayoyi na karatun Ƙur’ani da makarantun allo.

Ya ce kamfanin Mamuda babban kamfani ne da yake bada gudummuwa na samar da kayayyaki na amfanin yau da kullum da ake zuwa daga ƙasashe ake saye wannan abin alfahari ga jihar Kano da ƙasar nan.

Ya ce Mamuda mutum ne da yake taimako don Allah, tsohon ɗan kasuwa ne da ya soma da  harkar fata da buhuna, “ya shigo harkar kayan masarufi na yau da kullum da na ciye-ciye da lemuka da sinadaran wanka da wanki.”

Gaddafi Isyaku ya ce kamfanin Mamuda ya bai wa ‘yan asalin jihar Kano kaso 70 aiki, “domin yanzu haka akwai mutum 18,000 ‘yan asalin Kano da suke aiki wannan abin a jinjina masa ne.”