Game da kuskuren da sojoji suka yi kan masu Mauludi

Tare da ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Ba tun yanzu ba ake samun matsaloli na kuskuren aiki da sojoji ke yi yayin hare-haren da suke kai wa kan ’yan ta’adda a wurare daban-daban na arewacin ƙasar nan, abin da ke haifar da asarar ɗimbin rayukan waɗanda ba su ji ba, ba su gani ba.

Bincike ya nuna cewa, a dalilin irin wannan kuskure da sojoji ke yi an rasa rayukan ’yan Nijeriya aƙalla 425 tsakanin yara aanana, mata da maza, a lokuta daban-daban, daga shekarar 2017 zuwa 2023.

Wani rahoto da ke bayyana sakamakon binciken da wata ƙungiya mai suna SBM Intelligence ta gudanar game da rayukan fararen hula da ake rasawa na waɗanda da ba su ji ba ba su gani ba, wanda hare-haren jiragen yaƙin sojan sama na Nijeriya ke afkawa ba zato ba tsammani, an gano cewa an rasa rayukan fararen hula fiye da 300 tun daga shekarar 2017.

Waɗannan kura-kurai na faruwa ne a lokacin da sojojin ke cewa, suna farautar maɓoyar ’yan ta’adda ne da ke vuya a cikin dazuka da ƙauyuka, kuma a mafi akasarin lokuta babu wani abu da ake cewa game da rayukan da aka rasa. Kawai ana ɗaukar su a matsayin waɗanda tsautsayi ya bi ta kansu ne kawai. A cewar rahoton SBM Intelligence, akasari waɗannan kurakurai sun faru ne a cikin shekaru biyu na baya bayan nan. Jihohin Neja, Zamfara, Katsina, Nasarawa, Borno da Yobe su ne abin ya fi shafa.

A wata takarda da qungiyar Arewa Murya Ɗaya ta rabawa manema labarai an bayyana cewa a shekara 2021 sojoji sun kashe wasu masunta 20 a Jihar Borno a wani ƙauye da ke bakin iyakar Nijeriya, Nijar da Kamaru da Chadi ta dalilin wani hari da jirgin yaƙin sojojin ya kai, wanda kuma suka ce kuskure ne. Kwanaki 9 a tsakani sojojin sun sake kai wani hari kan wasu fararen hula a Jihar Yobe, inda aka samu asarar rayuka har mutun 9. A nan ma suka ce kuskure ne!

Na san ba za mu manta da wani hari da sojojin suka kai ba kan wasu ‘yan gudun hijira a Jihar Borno, wanda a nan har rayukan fararen hula 120 aka rasa a Borno sojojin sun ce kuskure ne,

Harin ranar Lahadi da jirgin yaqin rundunar Sojojin Ƙasa ta Nijeriya ta kai kan wasu ƙauyawa da ke gudanar da taron Mauludi a ƙauyen Tudun Biri da ke Ƙaramar Hukumar Igabi na Jihar Kaduna wanda aka ƙiyasta ya hallaka rayuka fiye da ɗari shi ne hari mafi muni da aka taɓa kai wa cikin kuskure, da ya girgiza arewacin ƙasar nan bakiɗaya.

Wannan mummunan hari ya jawo suka da la’anta daga shugabanni da talakawan ƙasa daga ɓangarori daban-daban a ciki da wajen ƙasar nan, saboda irin yadda abin ya faru ya nuna gazawa da lalacewar aikin tsaro a Nijeriya. Sojojin da muke alfahari da ƙoƙarinsu da ƙwazonsu wajen yaƙi da ɓatagari, a ciki da wajen ƙasar nan, sai ga shi yanzu sun koma kashe ’yan ƙasa, ‘yan’uwanmu, waɗanda ya kamata a ce suna aiki ne don tsare rayukansu da tabbatar da tsaron ƙasa.

Kodayake rundunar sojojin ƙasa ta yi gaggawar fitowa ta nemi afuwar ’yan Nijeriya bisa wannan mummunan kuskure, kuma abin takaici da kunya ga rundunar, tare da alƙawarin gudanar da bincike don gano waɗanda ke da hannu cikin harin da kuma tabbatar da ganin an biya diyyar rayukan da aka rasa, da ma ɗaukar nauyin jinyar waɗanda harin ya jikkata.

Har ma kuma mun samu rahoton ziyarar da Babban Hafsan Sojojin Ƙasa na Nijeriya Laftanar Janar Taoreed Lagbaja ya kai ƙauyen Tudun Biri, domin jajentawa al’ummar yankin da Gwamnatin Jihar Kaduna kan wannan mummunan al’amari, inda ya gana da shugabannin al’umma a yankin tare da ziyartar kabarin bai-ɗaya da aka binne waɗanda suka kwanta dama.

Mun ji fadar shugaban qasa ma tana jajentawa jama’ar Tudun Biri da al’ummar Musulmi kan tsautsayin da ya faru, da alƙawarin gano musabbabin wannan kuskure. Yayin da shi ma Ministan Tsaron ƙasa, Badaru Abubakar, tsohon Gwamnan Jihar Jigawa ya roqi gafarar ’yan Nijeriya game da al’amarin, da jaddada alƙawarin biyan diyya ga dukkan rayukan da aka rasa.

Amma ɓacin ran abin da ya faru ya harzuƙa ‘yan Arewa musamman al’ummar Musulmi da ke kallon al’amarin a matsayin ganganci da rashin nuna ƙwarewa, kan kuskuren da za a iya kauce masa. Malaman addini da sarakunan gargajiya, har da kungiyoyin al’umma na cigaba da nuna vacin rai da kiraye kirayen gwamnati da hukumomin rundunar soja su tabbatar an fito da masu hannu a wannan kisan gilla an hukunta su. Har ma da masu kiran da Ministan Tsaro Badaru Abubakar ya sauka daga muqaminsa saboda abin da ya faru babban abin kunya ne ga Nijeriya.

Wajibi ne a daidai nan, mu ƙara kira ga Babban Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Harkokin Tsaro Malam Nuhu Ribaɗu da lallai ya kafa kwamitin bincike cikin gaggawa, don gano masu hannu cikin wannan ɗanyen aiki, kuma a fito a yi wa jama’ar ƙasa bayani, domin kwantar da hankalin ‘yan ƙasa, saboda yanayin da jama’a ke ciki na harzuƙa da fushi. Lallai abin ban haushi ne da takaici a yayin da ’yan ta’addan Boko Haram ke dawowa da ta’addacinsu, ‘yan bindiga na cigaba da satar jama’a suna garkuwa da su a dazuka, amma a maimakon a ji cewa, jami’an tsaron Nijeriya na cin galabar su, sai gashi rayukan waɗanda basu ji ba, basu gani ba ne ke ƙara salwanta.

Kodayake a wani jawabi da Babban Hafsan Tsaron Ƙasa Janar Christopher Musa ya shaidawa tashar talabijin ta Arise TV cewa, sojoji sun kai hari ne bayan wani rahoton sirri da sojoji suka samu na cewa akwai wani shiri da wasu ’yan ta’adda ke yi na kai hari, wanda ya sa aka tura jirgin yaƙi mai leƙen asiri wajen da ake zaton ’yan ta’addan suna da sansani. Kuma sai aka ga jama’a zaune a ƙasan bishiya kamar yadda ’yan ta’addan daji suke yi, sannan an lura da kaiwa da komowar mutane a yankin wanda ya yi kama da na ‘yan ta’adda, don haka suka ɗauki matakin da ya kamata a lokacin. Sai daga baya suka gane an samu kuskure, ba inda ya kamata a kai harin aka kai ba!

Ko da mun amince cewa, kuskure ne, wanda yana iya faruwa a kowanne lokaci, amma a irin wannan lokaci babu wani abu da rundunar Sojojin Nijeriya za su iya faɗa jama’a su yi musu uzuri, saboda sanin irin gogewa da ƙwarewar da ake da aka san sojojin ƙasar nan da su. Sannan yadda abin ya faru dole ya harzuƙa jama’a, ta yaya za a ce jirgin yaƙi ya sake bam kan mutanen da ba sa riƙe da makami, suna zaune cikin natsuwa suna sauraren jawaban malamai kan tarihin rayuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAWA)?

Kuma ba tare da wani ya mayar da martani ba, jirgin ya sake dawowa lokacin da waɗanda suka kai ɗaukin gaggawa don ceton mutanen da harin ya rutsa da su, a sake sake musu wani bam ɗin? Ina jami’an leƙen asirin da ke taimakawa rundunar tsaro da bayanan sirri, ko suna nufin su ce ba tare da wani bayani a hukumance ba, haka kai daga ganin taron jama’a cikin dare sai su sake musu bam?

Ni dai ina da kokwanto kan haka. Lallai akwai wani abu a ƙasa da ya kamata a yi bincike a kai. Kamar yadda malaman addini irin su Khalifa Sanusi Lamiɗo Sanusi, da Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi da wasu malaman da ma ba na Ɗariƙar Tijjaniyya ba, irinsu Sheikh Sani Yahaya Jingir na Jos, da Sheikh Abubakar Salihu Zariya da ‘yan siyasa irinsu Sanata Shehu Sani, suke ta jan hankalin hukumomi kan wannan al’amari.

Muna fatan rundunar sojojin Nijeriya kamar yadda suka nuna gazawar su da bayar da haƙuri kan abin da ya faru, za su ɗauki tsauraran matakai, don hana sake aukuwar irin haka nan gaba.