Bom ɗin Tudun Biri ya jawo matuƙar juyayi

Tare da NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Haka rayuwa ta ke wataran a na kuka wataran a yi dariya amma gaskiya a yanayin da Nijeriya ke ciki mafi rinjaye ko ba kukan a ke yi ba to ba dai dariya a ke yi ba. Duk ƙaddarar da ta yi mai kyau ko mummuna sai a maida lamari ga Allah. Ɗan-adam ba shi da masaniyar abun da zai faru da ke ɓoye in ba sanar da shi a ka yi ba.

Haka nan ya fi ma alheri da Allah Maɗaukakin Sarki ya ɓoye ma na rana ko lokacin da za a karvi ran mu. Haƙiƙa rashin sanin lokacin tafiya ma wani arziki ne don haka mutum zai yi ‘yar rayuwar sa a tsanake ba muguwar fargaba. Kullum mutum zai fito daga gida ya yi addu’ar kariya daga Allah don ko tafiyar ta zo sai Allah ya hukunta mutum ya tafi a yanayi mai kyau. Da zarar ka shiga kafafen sadarwa yanzu na zamani za ka ga labarin mutuwa a wajaje daban-daban. Hotunan gawarwaki kuma sun zama ruwan dare.

Yau ko hatsarin mota a ka yi za ka ga wasu na ɗaukar hotunan waɗanda su ka riga mu gidan gaskiya su na yaɗawa. Ɗaukar gawa a bufe haka daga wajen hatsari ba daidai ba ne. Ba zan ce masu cigiyar wanda ya rasu da ba a san ‘yan uwan sa ko inda ya fito na aikata wani laifi ba. Cigaban zamani ya kawo hanyoyin sadarwa cikin sauƙi. Labarin mutuwa da a jerin labaru na kafafen labaru na ainihi na zuwa ne a ƙarshe matuqar ba mutuwar da ta shafi gari ko kasa ne gaba ɗaya ba kamar mutuwar shugabanni.

Don haka kafin a ɗau hotuna a suturta gawa tukun don wani lamarin ba ya ganuwa da sauƙi ga mutane da dama don tsananin tausayi ko juyayin yadda lamari ya afku.

Ƙungiyoyi da ɗaiɗaikun mutane na nuna juyayi da buƙatar bin kadun ma’abota halartar MAULIDI a Tudun Biri da ke yankin Igabi a jihar Kaduna da bom ɗin rundunar sojan Nijeriya ta hanyar tura jirgi marar matuƙi ya yi sanadiyyar mutuwar gommai a cikin su inda wasu da dama su ka samu raunuka.

Rundunar sojan Nijeriya a Kaduna ta hanyar gwamnatin jihar ta ɗau hauyin kai harin amma ta ce cikin kuskure ne.

Tun farko rundunar sojan saman Nijeriya ta nesanta kan ta daga harin duk da ta ce ba ita kaɗai ke amfani da jirage marar matuƙa a rundunonin tsaro a Arewa maso yamma ba.

Haƙiƙa faruwar wannan akasi ya jawo juyayi da kuma neman binciken yadda a ka samu kuskuren don kaucewa hakan a gaba.

Ƙungiyar ANSARUL DIN ATTIJJANIYYA da ke kula da ‘yan ɗarikar Tijjaniyya a Nijeriya kuma ke gudanar da Maulidi ta buƙaci ɗaukar matakan zahiri kan akasin da ya afku.

Babban sakataren ƙungiyar Mallam Alkassim Yahaya Yawuri ya ce su na buƙatar diyyar mutanen da a ka rasa da kula da jinyar waɗanda su ka samu raunuka.

Shi kuma wani zauren ‘yan Arewa mai masu sharhi ya nuna takaicin aukuwar harin da ya ce ba daɗin ji hakan ya fito daga waɗanda a ke ɗauka masu kare rayukan jama’a.

Muhammad Ibrahim Gamawa shi ne kakakin zauren ya na mai cewa sun yi Allah wadai da abun da ya faru. Gamawa ya ce an samu irin wannan akasi a zamanin gwamnatin Buhari na kuskuren hari kan fararen hula da ba su yi laifin komai ba ga shi hakan ya cigaba ƙarƙashin gwamnatin Bola Tinubu.

Irin wannan kuskure ba farau ba ne don a shekarun baya ma wani jirgin sojan saman Nijeriya ya sauke bom kan sansanin ‘yan gudun hijira a Rann da ke Borno inda kimanin mutum 50 su ka rasa ran su.

A irin hakan ba a samu wani matakin da ya wuce nuna takaici, neman afuwa da kuma alƙawarin ɗaukar matakan hana afkuwar hakan a gaba. Dama ai jami’an tsaro ne da a ka tura don kare lafiyar jama’a sai a ka wayi gari sun kai farmaki kan jama’ar bisa kuskure ko ganganci, zai yi wuya a ɗau wani tsatstsauran mataki a kai da ya wuce kiyaye hakan a gaba. In an rasa rai ai ba abun da za a yi a musanya shi da wani.

Fadar gwamnatin Nijeriya Aso Rock ta ce shugaba Bola Ahmed Tinubu zai ɗau matakan ladabtarwa kan duk wanda a ka samu da sakaci a harin bom daga jirgi marar matuƙi kan taron masu Maulidi a Tudun Biri da ke Igabi a jihar Kaduna.

Zuwa yanzu dai a na cigaba da samun kiraye-kiraye ga gwamnati ta tabbatar da gano haƙiƙanin wanda ya ba da umurnin kai harin da yadda har a ka kai hari kan ‘yan kasa masu taron ibadar su kuma ba tare da riƙe makami ba. Kazalika an samu masana tsaro da su ka zayyana yanda jirgi marar matuƙi ke aiki ta hanyar sarrafa shi daga kasa kuma ya na ɗauke da kamarar da kan tantance wajen da za a kai wa hari, don haka da mamaki a samu kuskure indai ba mummunar ƙaddara a ka samu ba. Kazalika matuƙar labarin kai hari na biyu bayan na farko a bigiren ya tabbata inda a duk biyun a ka samu asarar rayuka to akwai babban abun takaici a ciki da lalle a yi bincike na haƙiƙa don gano gaskiyar dalilan kai harin.

Mai taimakawa shugaba Tinubu kan labaru Abdul’ziz Abdul’aziz ya ce shugaba Tinubu ya yi magana kan akasin lokacin da ya ke kan hanyar dawowa daga Daular Larabawa bayan halartar taron nazari kan hanyoyin magance sauyin yanayi kuma ya yi matuƙar takaicin abun da ya faru.

A nan Abdul’aziz ya ce shugaban zai sa a gudanar da bincike kuma duk wanda a ka samu da laifi zai ɗanɗana kuɗar aikin sa.

Shugaban a saƙon ya yi ta’aziyya ga waɗanda su ka rasa ran su da kuma jajantawa iyalan waɗanda su ka rasa ‘yan uwan su; ya bayyana fara ɗaukar matakai na nan take kan akasin.

Duk da haka bayanin ya nuna jami’an tsaro na iya ƙoƙarin kakkave ‘yan ta’adda ne a lokacin da a ka samu akasin, amma hakan ka iya zama wani babban kuskuren aiki.

Babban hafsan sojan ƙasan Nijeriya Laftanar Janar Taoreed Labgaja ya ziyarci jihar Kaduna don jajanta harin da jami’an sojan su ka kai da jirgi marar matuƙi kan masu Maulidi a Igabi inda fiye da mutum 90 bisa alƙaluman da a ka fitar a daidai jana’izar su ka rasa ran su kuma da dama su ka samu raunuka.

Janar Lgbaja ya tsaya gaban babban ƙabarin da a ka binne marigayan bayan halartar jana’izar su. Ba daɗin gani yadda gawawwakin marigayan su ke inda zuciya mai rauni ma ba za ta iya kallo na biyu ga marigayan ba.

Wannan na nuna alamun akasin ya taɓa rundunar wacce ta amince da ɗaukar alhakin harin amma cikin kuskure.

Za a jira a ga irin binciken da rundunar za ta gabatar da ka iya kai wa ga ganewa ko akwai yiwuwar sakaci a harin ko ma dai aƙalla a kiyayi irin sa a nan gaba don hare-haren kuskure sun sha faruwa daga rundunar tsaron Nijeriya.

An ji mataimakiyar gwamnan Kaduna Hajiya Hadiza Balarabe na cewa zai yi wa gwamnatin jihar nauyi ta iya biyan diyyar marigayan bisa tanadin Musulunci ita kaɗai amma za ta hada kai da rundunar sojan da gwamnatin tarayya don samun abun da ya dace kuma ta na rokon yin haƙuri da abun da a ka samu.

Koma me za mu ce akwai sauƙi tun da soja sun dau nauyin harin amma bisa kuskure maimakon a ce ko ma ’yan ta’adda ne su ka kai harin tun da har wani labari kwanaki duk da jami’an tsaro ba su inganta shi ba na yadda barayin daji su ka harɓon jirgin soja a jihar Neja. Duk da an ga ɓarayin na nuna sassan jirgin ba lalle ba ne a ce harɓo jirgin a ka yi don zai iya yiwuwa ya samu matsalar inji ne a ka samu hatsarin.

Koma yaya za a ba da labarin ya na da ban tsoro da juyayi. Kuma ai in sojojin ba sa buƙatar ɗaukar nauyi za sui ya cewa ’yan bindiga su ka tashi jirgin marar matuqi da su ka samu ta wata hanya. Kullum ai mu kan ji labarin a na cewa makaman ’yan ta’addan sun fi na jami’an tsaron ƙasa inganci ko da kuwa ‘yan ta’addan ba su da ƙwarewa irin ta jami’an tsaron ƙasa.

Wani labarin na nuna ‘yan ta’adda ne daga wasu yankuna su ka kauro yankin na Igabi shi ya jawo amfani da jirgin marar matuqi.

Kammalawa;

Tun da Allah ya sa rundunar soja ta ɗau alhakin harin, to ya dace ta nuna tausayawa ta hanyar aiki da rundunar tsaro da gwamnatin Bola Tinubu wajen samar da diyya ga ‘yan uwan waɗanda su ka mutu da ɗaukar nauyin jinyar waɗanda su ka samu raunuka.

Mun ji labarin akwai wata mata ma da ta rasa ‘ya’yan ta gaba ɗaya da wani da duk gidan su su ka mutu a harin sauran shi kaɗai. Allah ya sa ba iyalin da za a samu duk ma sun koma ga Allah a harin don aƙalla a samu wanda za a ba wa diyya ko ma in bai yiwu ba a samu wanda za a yi wa ta’aziyya da tausaya ma sa ko da a kundin tarihi ne.