Rahoton bincike: Jihohi 10 da suka yi zarra wajen cin bashi a Nijeriya

Daga AMINA YUSUF ALI

A cikin shekarar bana ta 2023 Nijeriya ta fuskanci ƙalubale da dama da yake da alaƙa da tattalin arzikin ƙasar. Wannan dalili ya sa wasu jihohi da dama a Nijeriya suka dulmiya tsundum a cikin tarkon bashi. Jaridar Ingilishi ta The Spectacles ta yi bincike da nazari a kan wasu jihohi guda 10 da suka fi kowaɗanne ciyo bashi a Nijeriya.

  1. Legasa (Naira triliyan 1.97) Ta farko a cikin jerin ita ce jihar Legas wacce take a Kudancin Nijeriya. Jihar Legas ta jagoranci wannan jeri ne na jihohi masu kan bashi ne saboda bashin da ta kinkimo har na Naira tiriliyan 1.97. kodayake, wasu suna alaƙanta bashin da cewa ta aro shi ne don cigaba da wasu ayyukan more rayuwa da ba su kammalu ba saboda rashin kuɗaɗe da kuma cigaba da tafiyar da kasuwancin ƙasar nan kasancewarta babbar cibiyar kasuwanci ta ƙasa.
  2. Jihar Kaduna (Naira biliyan 525.9): Jihar Kaduna ita ce ta biyu daga jihohi goma masu kan bashin. A matsayinta ta biyu a jerin, ta lodi bashin kuɗi da ya kai Naira biliyan 525.9. Bashin jihar ana alaƙanta shi ne da harkar ilimi, harkar lafiya da kuma samar da ababen more rayuwa.
  3. Jihar Delta (Naira biliyan 511.3): Ita kuma jihar Delta ita ta ɗauki mataki na uku da lodin bashinta har na Naira biliyan 511.3. waɗannan kuɗaɗen da aka aro ana tsammanin jihar za ta yi amfani da su ne wajen wajen zuba jari a ɓangarorin da suka shafi man fetur da kuma ƙoƙarinsu na sabuntawa da qara yawan hanyoyin samar da kuɗin shiga a jihar.
  4. Jihar Ogun (Naira biliyan 379.2): Jihar Ogun ita ce ta zama ta huɗu da tarin bashin da ya kai har Naira biliyan 379.2. kuma ana tsammanin ta yi amfani da kuɗin da ta ranto ne wajen harkar masana’antu da kuma samar da ayyukan more rayuwa.
  5. Jihar Edo (Naira biliyan 325.1): Jihar Edo ita ce riƙe da kambun matsayi na 5 inda take ɗauke da lodin bashin Naira biliyan 325.1. bashin jihar ana alaƙanta shi ne da zamanantar da harkar noma da ilimi da raya birane.
  6. Kuros Ribas (Naira biliyan 322.0): Jihar Kuros ribas wacce ke da matsayi na 6 ita kuma ta kinkimo bashin Naira biliyan 322.0. kuma kuɗin da ta ciyo bashin ana sa ran an yi amfani da shi ne a harkar buɗe ido, noma da kiwo da ababen more rayuwa.
  7. Jihar Ribas (Naira biliyan 290.2): Jihar Ribas ita ce ta bakwai a jerin jihohin da suka fi kowa nauyin bashi a Nijeriya. Jihar Ribas na da dakon bashi har na Naira biliyan 290.2 wanda ake tsammanin jihar ta yi amfani da su wajen cigaba da ayyukan more rayuwa da kuma harkar albarkatun ƙasa a jihar.
  8. Jihar Imo (Naira biliyan 280.8): Jihar Imo da lodin bashi har na Naira biliyan 280.8 ta ɗauki matsayi na 8 daga jerin jihohi mafiya yawan bashi a Nijeriya. Amma ana tunanin an zuba waɗancan kuɗaɗe a harkar inganta harkar lafiya, ilimi, da kuma ayyukan more rayuwa.
  9. Jihar Bauchi (Naira biliyan 278.7): Bauchi ta ɗau matsayi na tara a jerin jihohi 10 mafiya cin bashi a Nijeriya. Jihar na da lodin bashi na Naira biliyan 278.7. Bashin ana tsammanin an zuba su a harkokin noma da kiwo, lafiya da kuma ilimi.
  10. Jihar Akwa Ibom (Naira biliyan 233.7) Jihar Akwa Ibom da lodin Naira biliyan 233.7 ta zama ta 10 daga jerin jihohi mafiya cin bashi. Bashin da jihar ta ciyo suna da alaƙa da ayyuka da aka yi a harkar man fetur da Gas da kuma ababen raya ƙasa.

Sai dai wani sharhi da rahoton binciken ya yi, ya bayyana cewa lodin bashin da yake kan waannan jihohi shi yake ƙara haska hoton irin yadda tattalin arzikin ƙasar Nijeriya ya taɓarɓare. A cewar rahoton, duk da dai cin bashin zai iya zama wata hanya ta samar da kayan cigaban ƙasa, amma samar da tsarin taka-tsan-tsan wajen kashe kuɗi yana da muhimmanci domin rashinsa zai iya jawo ƙalubale a harkar tattalin arziki a ƙasar.

Hakazalika kuma, sa ido da ɗaukar mataki a kan matsalolin da suke jawo cin bashin suna da matuqar muhimmanci a samar da daidaito a harkar tattalin arzikin jihohin har ma da ƙasar gabaɗaya.