Gwamnatin Tarayya ta ci burin ninninka kuɗin fetur zuwa Naira tiriliyan 7.69 a shekarar 2024

Daga AMINA YUSUF ALI

Gwamnatin Tarayya ta ci burin ninninka kuɗaɗen shiga da take samu ta hanyar man fetur har ninki uku wato zuwa Naira tiriliyan 7.69 a shekarar 2024 domin ta samu damar cikashe wani vangare na kasafin kuɗin ƙasa na shekarar 2024 wanda ya kai har kimanin Naira triliyan 27.5.

A cewar wani lissafi da hasashe a game da gabatar da daftarin ƙudurin kasafin kuɗin ƙasar nan na 2024 wanda ministan kasafin kuɗi da tsare-tsaren tattalin arziki, Abubakar Atiku Bagudu ya gabatar, ya nuna cewa hasashen kuɗin shigar da za a samu a ɓangaren man fetur a 2024 ya ɗara lissafin abinda aka saka a kasafin a kasafin kuɗi na shekarar 2023 har sau uku, wanda Naira tiriliyan 2.23 ne a wancan lokacin.

A taƙaice dai abinda wannan bayani yake nunawa shi ne, gwamnatin Tarayya ta ci burin ninninka kuɗin shiga har sau uku daga sashen da ƙalubalai sun riga suka gurgunta shi. Ƙalubalan sun haɗa da satar mai, rashin muhallai da kayan aikin gudanarwa, da sauransu waɗanda suka sa kuɗin shiga a ɓangaren tsahon shekaru yake ta yin ƙasa. Domin gwamnatin tana sa ran samun ƙarin kaso 41.98% na jimillar kuɗin shigar wato Naira tiriliyan 18.32 a shekarar 2024.

Kodayake, hasashen gwamnatin ya qara nuna cewa, akwai yiwuwar samun raguwar kuɗin shiga a ɓangaren man fetur ɗin a shekarun 2025 (Naira tiriliyan 6.83) da kuma 2026 (Naira tiriliyan 7.08), musamman idan aka kwatanta da abinda aka hasaso za a samu a shekarar 2024.

Sai dai kuma mai kamar zuwa akan aika. Alamar Juma’a mai kyau da Laraba ake ganewa. Domin ɓangaren man fetur a ƙasar nan yana matuƙar fuskantar ƙalubalai waɗanda da wahala a ce gwamnatin ta iya cika wancan buri nata na ninninka kuɗin shiga a sashen nan da shekarar 2024. Haka kuma alƙaluma sun nuna cewa koyaushe Gwamnatin tarayya tana kasa cimma burin cika adadin kuɗi ko man fetur da ta yi hasashen za ta samar daga sashen.

Babban misali yadda Kakakin majalisar wakilai ta Nijeriya, Honarabul Tajudeen Abbas ya yi wani jawabi na musamman a taron kwamitin wucin gadi na masu tattaunawa a kan matsalar satar man fetur.

Wannan kwamitin an kafa shi ne kuma an ɗora masa alhakin bincike a kan ta’azzarar satar mai ta bututu da kuma sama da faɗi da satar mai a ƙasar nan.

A cewar Honarabul Abbas, Nijeriya kan yi asarar sama da gangunan man fetur sama da 300,000 a kowacce rana tare da Naira tiriliyan 1.29 kowacce shekara saboda satar mai da sauran al’amura na laifuffuka.

Wannan ya sa a cewar sa gwamnatin ba ta taɓa cimma ko da kaso 80 cikin 100 na burin da take son ta cimma a kan man fetur. Don haka ake ganin da kamar wuya wannan buri na gwamnati a kan kuɗin shigar man fetur a shekarar 2024 ya cika. Amma lokaci ne alƙali.