Kisan masu mauludi: Za a hukunta masu hannu ciki – Tinubu

*A na cigaba da tir da kisan ’yan mauludi a Kaduna
*Za mu biya diyya, inji Gwamnatin Tarayya 
*Fasahar zamani za ta rage tashin boma-bomai – Amurka ga sojojin Nijeriya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar wa al’ummar ƙasar cewa duk wanda aka samu da hannu a harin bom da aka kai ƙauyen Tudun Biri wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 90 za a hukunta shi.

Shugaban Ƙasar ya kuma bayar da tabbacin cewa, za a kula da duk waɗanda abin ya shafa a ƙarƙashin shirin tallafi na Folako Initiative da za a fara a wannan watan.

A cewarsa, al’ummar yankin za su kasance al’umma na farko da za a sake ginawa ƙarƙashin sabon tsarin.

Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, wanda ya wakilce shugaban, ne ya bayyana hakan a jiya Alhamis jim kaɗan bayan ya ziyarci waɗanda lamarin ya rutsa da su a asibitin koyarwa na Barau Dikko da ke Kaduna, domin jajenta mu su bisa wannan mummunan lamari.

Ya kuma bayyana cewa, Gwamnatin Tarayya na ci gaba da jajircewa wajen yaƙi da ‘yan fashi a faɗin ƙasar.

Bugu da ƙari, Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta yi alƙawarin biyan diyya bisa waɗanda harin bom ɗin ya halaka, kamar yadda Ministan Tsaro, Muhammad Badaru Abubakar, ya sanar, sa’o’i kaɗan bayan Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bada umarnin gudanar da cikakken bincike kan harin.

Ministan ya bayyana cewa Ma’aikatar Tsaro da Gwamnatin Kaduna za su yi aiki tare wajen gudanar da bincike kan abinda ya faru a Ƙaramar Hukumar Igabi ta Jihar Kaduna.

Shettima ya ce, “Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya aike mu ne, domin mu jajanta wa mutanen Kaduna game da wannan mummunan al’amari da ya faru. Halin mutanen da ke tare da ni shaida ne a kan yadda lamarin ya taɓa shugaban ƙasa sosai.

“Shugaban Ƙasa ya ji daɗin abin da ya faru, za mu so mu tabbatar wa jama’a da gwamnatin jihar Kaduna cewa gwamnati za ta ɗauki matakan kariya da kiyaye muradun al’ummarmu.

“Za a kula da waɗanda abin ya shafa da kyau a ƙarƙashin shirin Fulako wanda za a fara daga wannan watan kuma wannan al’umma ce ta farko da za a sake ginawa a shiyyar Arewa maso Yamma.

“Za a ɗauki dukkan matakan da suka dace don tabbatar da cewa an daƙile makamancin hakan nan gaba. Gwamnati za ta bi diddigin lamarin kuma duk wanda aka samu da laifi za a hukunta shi yadda ya kamata.”

A na cigaba da yin tir da kisan:

A na cigaba da yin Allah-wadai da nuna tsananin alhinin mutuwar mutane 126 kawo yanzu a harin kuskuren da sojoji suka kai Tudun Biri, cikin Ƙaramar Hukumar Igabi, Jihar Kaduna.

Ƙungiyar Amnesty International ita ce ta tabbatar da mutuwar waɗannan adadi yayin da suka ziyarci waɗanda harin ya shafa a ranar Talata.

Wasu da suka tsira daga harin sun bayyana cewa, sau biyu sojojin na jefa musu bom.

A ranar Lahadin da ta gabata wani harin bom da sujoji suka yi nufin kaiwa a kan ‘yan ta’adda ya kuskure ya faɗa a kan taron jama’ar da ke gudanar da bikin maulidi a ƙauyen Tudun Biri da ke yankin Ƙaramar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna.

Lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama tare da jikkata wasu da yawa.

Tuni dai Rundunar Sojin Nijeriya ta ɗauki alhakin kai harin, inda Hukumar Bada Agajin Gaggawa, NEMA, ta faɗa a ranar Litinin cewa mutum 86 ne suka rasa rayukansu, sannan 66 sun tagayyara a iftila’in.

Wannan mummunan al’amari na ci gaba da shan suka musamman daga Arewacin Nijeriya, inda ɗaiɗaikun mutane da qungiyoyi da dama ke kira kan a binciko waɗanda ke da hannu a lamarin don su fuskanci hukunci.

Sarkin Musulmi, Sarkin Zazzau, Ɗahiru Bauchi, NEF, Izala, sun buqaci gwamnati ta biya diyya:

Sarkin Musulmi, shahararren malamin addinin Musulunci, Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi, Ƙungiyar Dattawan Arewa, Izala dukkansu sun yi allawadai da harin kuma sun roƙi Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya tabbatar da an gudanar da cikakken bincike tare da biyan diyya ga iyalan al’ummar Musulmin da sojojin Nijeriya suka kashe a harin bom ɗin na ranar Talata.

A jawabinsa yayin da yake zantawa da manema labarai a Bauchi, Shehin malami Ɗahiru Bauchi ya ce, “Muna so Gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ta jajirce wajen tabbatar da adalci ga waɗanda abin ya shafa da aka kashe a wajen bikin Mauludi, tare da hukunta jami’an da suka aikata wannan ta’asa.

“Ya kamata gwamnati ta yi aiki tuƙuru don hana abubuwan da ke faruwa a nan gaba, da kuma kiyaye rayukan ‘yan Nijeriya da yake salwanta?

“A kare musu mutuncinsu, kare haƙƙinsu na rayuwa a matsayinsu na ’yan Adam, a kare musu ’yancinsu na yin addininsu ba tare da tsangwama ba da kuma kiyaye haƙƙin ɗan adam da dokokin ɗan adam na duniya.”

Ya miqa ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan da ɗaukacin al’ummar Musulmin duniya da ma na Afirka, ya kuma yi addu’ar Allah Ya jiƙansu Ya gafarta musu, ya kuma ba mu haƙuri jure rashinsu.

Malamin ya ce, “Bai kamata a riƙa yin wasa da rayukan jama’a ba, mun buƙaci a gudanar da cikakken bincike a kan wannan bala’in da ya kashe mutane da dama da ba su ji ba ba su gani ba.”

Ya ce, “Mun fara tattaunawa da gwamnatin tarayya ta hannun Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro, ya kuma yi alƙawarin cewa za su tabbatar sun yi bincike tare da yin adalci ga waɗanda abin ya shafa idan shugaban ya dawo daga tafiyarsa.”

Ɗahiru Bauchi ya ce, gudanar da cikakken bincike kan tashin bom ɗin da aka ce ba gangan ba ne yana da matuƙar muhimmanci wajen daƙile yawan faruwar waɗannan haɗurra a nan gaba ta hanyar nazarin yanayin da ya haifar da wannan musiba, “domin a baya an kashe wasu Musulmin da ba su ji ba ba su gani ba a lokacin da suke kan hanyar komawa gida an kai musu hari aka kashe su a Jos da kuma hari na baya-bayan nan da suka jefa da bam din da ya kashe su ba za mu amince da hakan ba”.

Harin abin tashin hankali ne da ba a buƙatar faruwarsa – Hedkwatar Tsaro:

Hedikwatar Tsaron Nijeriya ta bayyana harin jirgi maras matuƙi a matsayin abin tashin hankali da ba a buƙatar faruwarsa.

A sanarwar da Daraktan Yaɗa Labarai, Manjo Janar Edward Buba ya fitar, an kai harin ne sakamakon bayanan sirrin da aka samu cewa akwai ‘yan bindiga a yankin.

Rundunar sojin ƙasar ta ce lokaci zuwa lokaci takan ƙaddamar da irin wannan hari kan ‘yan bindiga da a wani lokacin yake shafar al’ummar gari.

Tuni dai Gwamnan Jihar Kaduna Uba Sani ya bada damar gudanar da bincike kan lamarin.

“Gwamnatin jihar ta aike da manyan jami’anta don tantance halin da ake ciki, da bayar da tallafi ga iyalan waɗanda abin ya shafa, da kuma ba da shawara kan ɗaukar matakan gaggawa don rage musu raɗaɗi.

“Ina tabbatar wa ‘yan jihata cewa har yanzu kariyarsu ce abin da muka fi bai wa fifiko a yaqin da ake yi da ta’addanci da ‘yan fashi da masu aikata laifuka a jihar,” inji Gwamna Uba Sani.

Haka nan Gwamna Sani ya yi kira da a kwantar da hankula tare da yin kira ga jama’a da su ci gaba da marawa jami’an tsaro da gwamnatin jihar baya a yaƙin da suke yi da masu aikata laifuka.

Harin ba kuskure ba ne — Sheikh Gumi:

Shi ma fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya yi zargin da gangan jirgin sojoji ya kai harin bom kan masu taron Mauludin.

Sheikh Gumi ya ce idan har harin bom na farko da jirgin sojan ya aka kai wa masu Mauludin kuskure ne, to me ya sa bayan minti 30 suka jefa bom na biyun a kan masu aikin ceton waɗanda aka jefa wa bom ɗin farko?

Ya bayyana cewa “Mutanen sun ce bayan an kai wannan hari an kashe mutane, sun je suna ƙoƙarin kwashe waɗanda suka rasu, sai bom na biyu ya sauka. Idan bom ɗin farko kuskure ne, baom na biyu kuma fa?

“Muna kuma fatan waɗanda suka rasu sun yi shahada, amma kada wani ya faɗa min cewa wai kuskure ne, a’a da gangan ne. Don haka duk wanda ya jefa wannan bom ya kamata a fito da shi.”

Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana haka ne a majalisin karatunsa a Masallacin Sultan Bello da ke Kaduna.

Malamin ya ce ko a lokacin yaƙi ba daidai ba a kai wa mata ko ƙananan yara ko tsofaffi  hari, amma duk da haka sojoji suka kai musu hari, bisa zargin iyalan ’yan ta’adda ne.

Ya ce abin da ya faru a Tudun Biri, Allah ne Ya fallasa irin varnar da sojoji suke aikatawa a cikin dazuka a yaƙin da suke yi da ’yan ta’adda.

Sheikh Gumi ya ce, “Mutane da yawa an kashe su a baya babu wanda ke magana har sai da harin ya zo kusa da gari.

“Na sha faɗi cewa duk abin da ke tsakaninmu ko ’yan fashin daji ko Boko Haram akwai buƙatar sulhu, amma wasu na cewa a’a a kashesu.

“A wannan ƙasar babu wanda zai faɗa min. Na yi ƙoƙarin nemo mafita amma an qi goyon bayanmu. Gwamnatin wani lokaci tana tunanin yaƙi, wani lokacin kuma sulhu.

“Waxannan mutane sun taru mata da yara, amma jirgin wanda ke da kemara ya je, kuma sun ga mutanen, amma suna tunanin mata da yaran waɗancan mutanen ne. Kuma da a ce hakan ne da kuma shiru za ku yi.

“Amma da yake an samu kuskure an kashe waɗanda ba su ake son kashewa ba. Mu a wurinmu ba mu son a kashe kowa, saboda harum ne kashe mata da yara da tsofaffi. Kuma ba mu goyon bayan irin hakan ko da kuwa ’yan IPOB ne.

“Muna kuma fatan wadanda suka rasu sun yi shahada, amma kada wani ya fada min cewa wai kuskure ne, a’a da gangan ne. Don haka duk wanda ya jefa wannan bom ya kamata a fito da shi.”

Kisan ba zai dakatar da mu wajen yaƙar ‘yan ta’adda ba – Ministan Tsaro 

Ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya sha alwashin cewa kisan da aka yi wa masu Mauludin bisa kuskure, ba zai dakatar da yaqi da ayyukan ta’addanci ba.

Ministan ya yi wannan alƙawarin ne a lokacin da ya ziyarci waɗanda harin ya rutsa da su a Asibitin Barau Dikko a Kaduna ranar Laraba. 

Matawalle, tare da babban sakataren ma’aikatar, Dr Ibrahim Kana, sun jagoranci wata babbar tawaga zuwa jihar Kaduna domin isar da jajentawar gwamnatin tarayya ga waɗanda abin ya shafa.

Mista Henshaw Ogubike, Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na ma’aikatar ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a Abuja.

Yayin da yake tofa albarkacin bakinsa, ministan ya bayyana cewa za a ci gaba da yaƙi da ta’addanci.

Ya ƙara da cewa, wannan mummunan lamari ba zai sa gwamnati ta hana yaƙi da ta’addanci ba.

“Ba za mu ja da baya a yaƙin da muke da ta’addanci ba saboda dole ne a fatattaki waɗannan masu aikata laifuka.

“Za mu ci gaba da yaƙar masu laifi har sai mun yi nasara a kan ‘yan fashi da sauran miyagun laifuka a ƙasar nan.”

Matawalle, wanda shi ma yana Asibitin Koyarwa na Barau Dikko da ke Kaduna, inda ake kula da waɗanda suka jikkata, ya bayyana cewa ziyarar ta biyo bayan umarnin Shugaba Bola Tinubu ne.

Ya kuma tabbatar wa gwamnatin jihar Kaduna ƙudirin gwamnatin tarayya na tallafa wa iyalan waɗanda abin ya shafa.

Rashin tsaro na ci gaba da janyo ɓarna a Nijeriya – Obi

Ɗan takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar Labour Party, LP, a zaɓen da ya gabata, Mista Peter Obi, ya bayyana matsalar rashin tsaro a ƙasar a matsayin abin takaici, yana mai cewa dagewar da ta yi a yanzu ya janyo wa Nijeriya varna.

Obi wanda ke mayar da martani kan harin da sojoji suka kai ta sama da ya hallaka mazauna ƙauyen Tudun Biri da ke jihar Kaduna, ya bayyana yadda rashin tsaro ke janyo asarar rayuka da dama.

Martanin nasa na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da aka fitar a shafin X, wanda aka saki ranar Talata.

Tsohon gwamnan jihar Anambra ya buƙaci sojoji da su yi taka-tsan-tsan da sanin makamar aiki don kauce wa irin wannan abin kunya ga sojoji da kuma ƙasa baki ɗaya.

A cewarsa, “duk wani lamari da zai haifar da cutarwa ko asarar rayukan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, ya kamata a kiyaye su.”

Fasahar ‘AI’ za ta rage tashin boma-bomai – Amurka ga Sojojin Nijeriya:

Hukumar Kula da Makamai da Tsaro ta Amurka ta faɗa a ranar Alhamis cewa tura jami’an leƙen asiri na mutum-mutumi wato ‘Artificial Intelligence’ zai taimaka wa sojojin Nijeriya wajen rage yawan hare-haren bama-bamai a ƙasar.

Jaridar Manhaja ta ruwaito cewa an samu sama da sau 12 na hare-haren da sojoji suka yi bisa kuskure, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar fararen hula sama da 400 da ba su ji ba ba su gani ba tsakanin shekarar 2017 zuwa 2023.

Cibiyar ta yi nuni da cewa karɓar AI da sojojin Nijeriya suka yi ba wai kawai zai inganta ƙarfinta ba ne, har ma zai hana sojoji karyar dokokin ƙasa da ƙasa.

Babban Mataimakin Sakataren Cibiyar, Paul Dean, ne ya bayyana hakan yayin wani taron tattaunawa da zaɓaɓbun ‘yan jarida a Abuja ranar Alhamis.

Ya ce, “Don haka da farko, mu jajanta wa wannan bala’in da ya faru a cikin wannan mako. Ina tsammanin tambayarku ta tayar da muhimmin batu cewa basirar wucin gadi za ta taimaka wa sojoji su inganta ayyukansu ta hanya mai ma’ana.

“Bayanan sirri na wucin gadi za su taimaka wa sojoji su aiwatar da ayyukansu na dokokin jinƙai na ƙasa da ƙasa. Zai taimaka sojoji su inganta inganci, kawar da son zuciya, da haɓaka yanke shawara gabaɗaya.

“Kuma wannan, ina tsammanin, zai yi matukar amfani ga zaman lafiyar duniya. Muna so mu ƙarfafa kyawawan aikace-aikace na basirar wucin gadi a cikin soja.

“Wannan shirin da mu da abokan akinmu suka ƙaddamar a watan da ya gabata ya ta’allaƙa ne kan cimma wannan kawai, ƙara girman darajar bayanan sirri a aikace-aikacen soja.

“Kuma a lokaci guda, tabbatar da al’ummomin ƙasa da ƙasa sun yi haɗin gwiwa tare da jerin ƙa’idoji na alhaki don tabbatar da cewa muna rage hadarin sakamakon da ba a yi niyya ba ko aikace-aikace mara kyau.

“Don haka muna da yaƙinin cewa lokacin da jihohi suka ba da kansu don amfani da wannan fasaha ta hanyar da za a iya gani, a bayyane, kwanciyar hankali, da kuma al’ada, al’ummomin ƙasa da ƙasa za su kasance cikin yanayin da za su iya ƙara yawan fa’ida tare da rage kasadar hanyar da ba ta dace ba.”

Dean ya kuma ce ƙungiyarsa a shirye take ta haɗa kai da gwamnatin tarayya domin daƙile yaɗuwar makamai da alburusai a ƙasar.

Ya ce, “Kuma a haqiqa, aikin ofishinmu yana cikin cikakken yanayin daƙile rikici, inganta zaman lafiya, da kafa ƙa’idojin da suka dace a fannin soja. Kuma ina ganin wannan ya sa mu dace da abokan zamanmu a nan Nijeriya.”

Haka zalika Amurka ta ce za ta taya sojojin Nijeriya rage yawan harin bom bisa kuskure da sojojin ƙasar ke kai wa fararen hula.