Tudun Biri: Sanatoci sun sadaukar da albashinsu na wata guda ga waɗanda harin bom ya shafa

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

Baki ɗayan sanatocin Tarayyar Nijeriya su 109 sun yanke shawarar sadaukar da albashinsu na wata guda da ya kai Naira miliyan 109 ga waɗanda iftila’in harin bom ya shafa a Tudun Biri, cikin Ƙaramar Hukumar Igabi, Jihar Kaduna.

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin ne ya bayyana haka ranar Lahadi a Fadar Gwamnatin Jihar Kaduna yayin da ya jagoranci tawagar Majalisar Dattawa zuwa jihar don miƙa ta’aziyya da kuma jajantawa.

Gwamnan Jihar, Sanata Uba Sani, shi ne ya tarbi tawagar yayin ziyarar.

Cikin sanarwar da ya fitar ta hannun hadiminsa Ismail Mudashir, Sanata Barau ya ce za a aika wa Gwamnan jihar da kuɗin domin isar da saƙo ga waɗanda aka yi domin su.

Gwamna Sani ya nuna godiyarsa dangane da wannan taimako da sanatocin suka yi don amfanin talakawansa.

Yayin ziyarar, sanatocin sun ziyarci waɗanda ke jinya a Asibitin Barau Dikko da ke jihar.

Tawagar sanatocin ta haɗa da Sanata Micheal Opayemi Bamidele; Sanata Ali Ndume; Sanata Abba Moro; Sanata Kamorudeen Olarere; Sanata Abdulhamid Malam-Madori; Sanata Aliyu Ikra Bilbis.

Sauran su ne, Sanata Ibrahim Bomoi; Sanata Ibrahim Lamido; Sanata Abdulaziz Yar’Adua; Sanata Victor Umeh; Sanata Muntari Dandutse; Sanata Lawal Usman da kuma Senator Emmanuel Udende.

By Editor