Shugabanci nagari ne kaɗai hanyar magance matsalar juyin mulki – ECOWAS

Shugaban Ƙungiyar ECOWAS, Bola Tinubu, ya roƙi shugabannin ƙasashen yammacin Afirka da su ba da fifiko wajen gudanar da shugabanci nagari da samar da walwalar jama’a, a matsayin wani muhimmin makamin yaƙar juyin mulki a yankin.

Da yake jawabi a wajen taron ECOWAS karo na 64 da ya gabata a ranar Lahadi, shugaban ya bayyana gudanar da shugabanci nagari a matsayin wani babban ginshiƙi na samar da goyon bayan jama’a ta hanyar kawo sauyi ga al’umma da tattalin arziki da cigaban yammacin Afirka.

“Samar da shugabanci nagari ba wai kawai zallar nasarar samin shugabanci ba ce, hanya ce ta magance matsalolin da ke damun ýan ƙasa da inganta rayuwarsu, da samar da ingantaccen yanayi da zai dace da samun ci gaba mai ɗorewa.

“Ta hanyar samar da kyakkyawan shugabanci kaɗai ne za a magance ƙalubalen talauci da rashin daidaito da sauran matsalolin da ke damun al’umma, da za mu daure mu ɗauki wannan hanyar da mun yi nasarar magance wasu daga cikin dalilan da suke bai wa sojoji damar shiga ayyukan farar hula a yankinmu,” in ji Shugaba Tinubu