Fitacciyar ma’aikaciyar NTA, Aisha Bello ta kwanta dama

Daga BASHIR ISAH

Allah Ya yi wa fitacciyar ma’aikaciyar tashar talabijin ta tarayyar (NTA), Aisha Bello Mustapha, rasuwa.

A ranar Lahadi Aisha ta rasu amma sai a Litinin aka yaɗa batun rasuwar wanda ya zuwa haɗa wannan labari ba a bayyana abin da ya yi ajalin marigayiyar ba.

A halin rayuwarta, marigayiyar ta yi fice musamman a fagen karanta labatai a tashar NTA.

‘Yan ƙasa da dama sun bayyana kaɗuwarsu game da Aisha duba da irin gudunmawar da ta bayar ga ɓangaren yaɗa labarai.

Da misalin ƙarfe ɗaya na ranar Litinin aka yi wa marigayiyar sallar janaza a Babban Masallacin Ƙasa da ke Abuja, kafin daga bisani aka tafi da ita makwancinta.