Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
‘Yan Majalisar Dattawan Nijeriya 109 sun sanar da sadaukar da albashinsu na wata guda ga dangin mutanen da harin kuskuren da rundunar sojin Nijeriya ta kai garin Tudun Biri, da ke Ƙaramar Hukumar Igabi, a jihar Kaduna ya yi ajalinsu.
‘Yan Majalisar sun ce za a yi amfani da kuɗin, da yawansu ya kai Naira miliyan 109, wato miliyan guda daga kowanne sanata domin hidimtawa mutanen, da zummar rage masu raɗaɗin halin da suke ciki.
Sanata Ali Ndume, mai tsawatarwa a majalisar dattawan Nijeriyar, wanda kuma ke cikin ‘yan Majalisar da suka ziyarci jihar ta Kaduna a ranar Lahadi don jajantawa mutanen, ya shaida wa BBC cewa, an riga an yi asarar rai, amma akwai buƙatar a taimaka wa iyalan mamatan.
Ya ce, “ Za a ba wa gwamnan jihar Kaduna kuɗin, domin ko da muka kai masa ziyarar jaje mun fahimci cewa shi ma ya damu ƙwarai da gaske a kan taimakon da ya kamata a yi wa irin waɗannan mutanen.”
‘Yan majalisar sun kuma nanata aniyar ganin an gudanar da sahihin bincike, don gano yadda lamarin ya faru, da kuma hukunta waɗanda bincike ya tabbatar da akwai hannunsu.
Ya ce,”Mun amince a binciki yadda wannan hari ya faru, domin ni a iya sanina irin wannan kuskuren kai wa mutanen da ba su ji ba su gani ba hari da sojojin Nijeriya suka yi ya kai 16.
“A jihata Borno, an sha samun irin wannan harin,” in ji shi.
Sanata Ali Ndume, ya ƙara da cewa irin waɗannan hare-hare sun zamo abin damuwa domin ba sau ɗaya aka tava samun irin haka ta faru ba, kuma mutanen da aka kashe a irin waɗannan hare-haren kuskuren jimillarsu ya kusa kai wa 500, a cewarsa.
“Don haka bai kamata a ci gaba da kai irin waɗannan hare-hare ba, saboda jami’an tsaro an san aikinsu shi ne tabbatar da tsaro da kare rayukan al’umma, amma kuma su zo suna kai irin waɗannan hari, zai zama ke nan kwalliya ba ta biya kuɗin sabulu ba aikin da suke ke nan.”
Ndume ya ce, “Ina tabbatar da cewa mu ‘yan majalisa za mu yi iya bakin ƙoƙarinmu don ganin an binciki wannan lamari da kuma tsayar da shi saboda gaba.”
Ya ce binciken da ya kamata a yi tare da bayar da shawarar ɗauko masu bincike masu zaman kansu kuma ƙwararru su gudanar da bincike a kan harin, sannan a yi binciken da wuri kuma a gani a ƙasa.
