Makarantar Ihya’us-sunnah ta yaye ɗalibai bakwai karo na farko a Legas

Spread the love

Daga DAUDA USMAN a Legas

Makarantar Ihya’us-sunnah Islamiyya a unguwar Mile-12 Intanashinal Market dake cikin birnin Legas a ƙarƙashin jagorancin shugaban kwamitin makarantar Alhaji Salisu Madobi Mai Barkono ta gudanar da taron walimar yaye ɗalibai maza da mata bakwai karo na ɗaya a Legas tare da neman taimakon zunzurutun kuɗi har Naira miliyan ashirin domin kammala ginin makarantar tare da faɗaɗa a zuzuwanta da sauran harkokin ayyukanta bakiɗaya.

Taron walimar yaye ɗaliban wanda ya gudana a makarantar Maidan Primary School dake unguwar Mile-12 ranar Lahadin makon jiya, manyan baqin malamai a wajen taron walimar sun haɗa da shugaban ƙungiyar Izala na jihar Legas Sheikh Imam Suleiman Ibrahim da limamin masallacin Juma’a na unguwar Mile-12 Sheikh Malam Buhari Yakubu da shugaban majalisar malamai na ƙungiyar Izala a jihar Legas Shekh Malam Muhammed Abubakar Arugungu da sauran manyan malamai maka mantansu.

Mahalarta taron walimar yaye ɗaliban sun haɗa da dukkan shuwagabanni da malaman makarantun Islamiyoyin daban-daban na jihar Legas da ‘yan kasuwa da sauran al’ummar Musulmin Kasuwar Mile-12 Intanashinal Market baki ɗaya Sheikh Malam Ibrahim Aliyu na’ibin limamin masallacin Juma’a na ‘yan Izala Mile-12 shi ne ya buɗe taro da addu, a Alhaji Auwalu tufak agege shi ne ya wakilci Alhaji Ali zanna da sauran iyayen makarantar a wajen taron walimar.

Tun bayan buɗe taro da addu’a ne aka ummurci Malam Abubakar limamin masallacin Juma’a na unguwar Hausa layi ya wa’azantar da al’ummar Musulmi bisa kan muhimmancin aikata ayyukan alheri a duniya baki ɗaya sannan aka ummurci ɗaliban maza da mata waɗanda suka samu nasarar sauke Alƙur’ani mai tsarki suka karanto waɗansu daga cikin ayoyin Alƙur’ani gwargwadon a bin da ya sauwaƙa.

Haka zalika shuwagaban nin makarantar suka bama Alhaji shehu usman jibirin samfam shugaban kasuwar Mile-12 Intanashinal Market da wadan su malamai lambar yabo tare da karramasu a koqarin su na kawo cigaban makarantar baki daya haka kuma aka kad damar da gidauniyar neman taimakon zun zurutun Kudi har naira milyan ashirin domin kammala ginin makarantar tare da faɗaɗa zuzuwanta dama sauran har kokin ta na yau da kullum.

Shi ma a nasa tsokacin a wajan taron walimar, shugaban kwamitin makarantar Alhaji salisu madobi inda bayan ya kammala nuna farin cikin sa tare da isar da godiyar sa ga Allah ubangiji suba hanahu wata ala daya basu dama tare da ikon gudanar da wannan taro na walimar yaye ɗaliban wannan makaranta yayima manyan baki fatan alheri na komawar su gidajensu lafiya.

By Editor