Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Hukumar Ƙwallon Ƙafar Ƙasar Kamaru, ta ƙi amincewa da buƙatar ajiye aiki da tsohon ɗan wasan gaba na ƙasar, Samuel Eto’o, ya gabatar mata.
A ranar Litinin ne, Eto’o ya miƙa takardar ajiye muƙamin shugabancin hukumar, yayin wani taron ganawa da aka gudanar a birnin Yaounde.
Tsohon ɗan wasan na Kamaru ya ce matakin nasa ya biyo bayan gazawar ’yan wasan ƙasar na ƙasa taɓukawa a gasar kofin nahiyar Afirka ta AFCON da ke gudana a ƙasar Ivory Coast.
Sai dai mambobin hukumar sun ce suna da qƙwarin gwiwa a kansa na ci gaba da aiwatar da sauye-sauye da kuma samar da cigaba ga vangaren ƙwallon qiafar ƙasar a kowanne mataki.
Ɗan wasan wanda ya taɓa lashe gwarzon ɗan ƙwallon Afirka har sau huɗu, ya samu cikakken goyon baya daga ɓangarori da dama, duk da cewa ya fuskanci suka game da yadda yake tafiyar da shugabancin hukumar da kuma zargin rashawa a shekarar bara.
Hukumar ƙwallon ƙafa ta nahiyar Turai CAF, yanzu haka tana gudanar da bincike kan abin da ta kira zarge-zarge masu tsauri daga manyan masu ruwa da tsaki na ƙasar Kamaru da suke yiwa Samuel Eto’o.
Hukumar ta lura da cewa, tsohon ɗan wasan na Barcelona da kuma Inter Milan, har yanzu babu wani laifi da aka same shi da shi, sai dai nan gaba idan an kammala bincike.
