Ƙungiyar Zaɓi Sonka ta yi gagarumin taro a Dutsen-wai

Spread the love

Daga ISAH GIDAN ƁAKKO a Zariya

A ranar Lahadin makon jiya, ƙungiyar zaɓi sonka da taimakon juna reshen shiyya ta ɗaya a jihar Kaduna suka yi wani babban taro da shugabanni da kuma mabobin ƙungiyar da suka fito daga kananan hukumomi takwas na shiyya ta ɗaya suka halarta da taron ya gudana a garin Dutsen Wai ta ƙaramar hukumar Kubau.

A lokacin wannan taro na tsawon yini guda, mahalarta taron da suka haɗa da shugaban ƙungiyar a shiyya ta ɗaya Injiniya Garba Bala, kyauta ba ta hana arziki, Ramin Kura da Sakataren ƙungiyar Alhaji Ɗanjuma mai nama furana da kuma maajin ƙungiyar na jihar Kaduna Alhaji Usman Tanimu mai TV da Rediyo, Babban Dodo, Zariya, duk sun halarta.

A likacin taron,sun tattauna matsalolin da suka dabaibaye ƙungiyar da rashin halartar taron da ƙungiya ke kira da kuma matakan da za a bi, domin bunƙasa ƙungiyar, fiye da yadda ta ke a yau.

A dai lokacin wannan taron mahalarta taron, sun bayar da kyawawan shawarwari na in an bi shawarwarin, a cewar mahalarta taron, matsalolin a ɗan ƙanƙanin lokaci, za su zama tarihi.

Tsaftace amfani da intanet: Kungiyar NADIR ta yi na’am da yunƙurin NITDA

Hedikwatar tsaro ta gargaɗi ƙungiyar HURIWA kan rikicin Filato

Mahalarta taron sun kuma ba junansu shawarwain ƙara tashi na halartar tarurrukan da ake shirya wa ƙananan hukumomi da na shiyya ta ɗaya da kuma halartar taron jiha a duk lokacin da aka kira.

A ƙarshen taron, bisa shugabancin uban ƙungiyar a shiyya ta ɗaya Alhaji Ubal Mutawallen Turawa kuma sarkin noman Turawa, sun yi kira ga sauran mambobin ƙungiyar da ba su sami damar halartar wannan taron ba, da lallai su halarci na shiyya ta ɗaya da zai gudana a garin Dutsen wai a cikin wata na Fabrairun wannan shekara ta 2024.

By Editor