Gwamnati na shirin farfaɗo da shirin bada tallafi na ‘Direct Cash Transfers’

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

Gwamnatin Tarayya za ta farfaɗo da shirin bada tallafin da aka fi sani da ‘Direct Cash Transfers’ wanda gwamnatin baya ta samar domin tallafa wa masu tsananin buƙata a faɗin ƙasa.

Ministan Kuɗi, Wale Edun ne ya bayyana haka sa’ilin da yake jawabi a wajen wani taro da aka shirya ranar Laraba a Uyo, babban birnin Jihar Akwa-Ibom.

A cewar Ministan, “Kwamitin shugaban ƙasa kan shirye-shiryen bada tallafi ya shirya ganin Shugaban Ƙasa inda zai gabatar masa da buƙatar sake farfaɗo da shirin bada tallafi ga masu tsananin buƙata. Ana yin dukkan mai yiwuwa domin rage wa ‘yan ƙasa rarɗaɗi.

“Muna sane da cewa akwai mutum kusan miliyan uku da ke cin gajiyar shirin a halin yanzu, amma duba da ƙarin da aka samu, akwai ƙarin mutum miliyan 12 da za su ci gajiyar shirin,” in ji Ministan.

Ya ƙara da cewa, “Muna da ƙwararru a fannin fasaha, ƙoƙarinmu shi ne mu ga an yi amfani da fasaha wajen tafiyar da shirin cikin lumana.”

Ya ce bayan kammala dukkan tsare-tsare, shirin bayar da tallafin zai ci gaba.

By Editor