Falastinawa a Gaza na fama da matsananciyar yunwa – Ofishin jakadancinsu a Nijeriya

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ofishin Jakadancin Falastinu a Nijeriya ya bayyana cewa, a rana ta 167 na yaƙin kisan ƙare dangi da ake yi wa al’ummar Falastinu, mutanen Gaza mata da qananan yara na fama da matsananciyar yunwa, rashin ingantaccen kiwon lafiya da sauran wahalhalu.

Jakadan Falastinu a Nijeriya, Abu Shawesh ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Alhamis. 

Sanarwar ta ce, “Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, Antonio Guterres da Babban jami’in kare haqqin bil’adama na Majalisar Ɗinkin Duniya Volker Turk sun bayyana irin matsananciyar wahalar da ake fama da ita a garin Gaza sakamakon hare-haren Isra’ila, wanda hakan ya hana shigarwa da rarraba kayan agaji da tafiyar da sauran hada-hadar kasuwanci a ƙasar Falastinu.”

“Kashi 100 na al’ummar Gaza na fama matsanancin ƙarancin abinci. Wannan shi ne karo na farko da matsalar ta shafi dukka yawan jama’ar garin.”

“A ranar Laraba, 20 ga Maris, 2024 adadin Falastinawa da aka kashe Gaza ya kai 31,819, yayin da 73,934 sun jikkata, sannan kimanin mutum 8,500 sun ɓace ɓat ba tare da an san inda suke ba,” inji sanarwar.

Ta ce, “baya ga kisan kiyashi da yankin Gaza ke fuskanta daga Isra’ila, yankin na kuma fama da matsanancin ƙarancin abinci, wanda a cewarsa wannan shi ne irinsa na farko da aka samu wata al’umma ta fuskanci matsalar rashin abinci makamancin haka.”

“Akwai ’yan gudun hijira 700,000 da suka fake a kashi 20 kacal na yankin Zirin Gaza.”

By Editor