Ramadan: Dubban ‘yan Nijeriya za su rasa Umara sakamakon matakin hana biza da Saudiyya ta ɗauka — Rahoto

Daga BASHIR ISAH

Akwai yiwuwar bana ‘yan Nijeriya da dama ba za su samu yin Hajjin Umar ba a wannan wata na Ramadana.

Hakan ba ya rasa nasaba da matakin da Ƙasar Saudiyya ta ɗauka na dakatarwa ko taƙaita da bayar da bizar zuwa yin Umara a ƙasar.

Wannan al’amari ya tada hankalin jama’a musamman masu niyyar zuwa Umara domin ninka ibadarsu a watan Azumin Ramdan.

Haka su ma kamfanonin shirya tafiye-tafiye zuwa Hajji da Umara sun nuna damuwarsu kan matakin wanda tuni ya haifar musu da asara sakamakon sauke musu bukin na masaukan da suka kama a biranen Makka da Madina.

Bayanai sun ce sabuwar dokar biza da ƙasar ta Saudiyya ta samar, ita ce ummul aba’isin haifar da jinkiri wajen bayar da bizar.

Kuma duk da ƙoƙarin da kamfanonin sufuri suka yi da kuma tattaunawa a tsakaninsu da Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON), har yanzu da yawan maniyyata Umarar sun kasa samun biza.

Shugaban Ƙungiyar Kamfanoni Masu Jigilar Maniyyata Hajji da Umara na (AHUON), Alhaji Yahaya Nasidi, ya yi hasashen cewa kashi 90 cikin 100 na maniyyatan Umara daga Nijeriya ba za su samu tafiya Umara ba saboda rashin biza.

Majiyarmu ta ce Saudiyya ta ɗauki matakin taƙaita ba da biza ne yayin watan Ramadan domin rahe cunkoso da kuma tabbatar da walwalar jama’a a masallacin harami da kewaye.