’Yan sanda sun yi karar Jaruma Amal kotu bayan kotu ta wanke ta

Daga AISHA ASAS 

Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya Shiyya ta Ɗaya (wato Zone 1) ta kai ƙarar fitacciyar jaruma a Kannywood, Amal Umar, gaban kotu kan zargin bayar da toshiyar baki ga wani ɗan sanda da ke binciken ta kan zargin aikata wata almundahanar kuɗi da ake zargin da sa hannunta a ciki, duk da cewa, kotu ta wanke jarumar tun a watannin baya.

A jiya Alhamis ne aka gurfanar da jarumar a kotun Majistare mai lamba 24 da ke Jihar Kano. 

Da yake jawabi a gaban manema labarai, Kakakin Rundunar ‘Yan Sanda Na Shiyya Ta Ɗaya, CSP Bashir Muhammad, ya bayyana cewa, Jaruma Amal ta yi yunkurin bayar da cin hanci ne ga wani ɗan sanda mai binciken almundahanar kudi da ake zargin wani saurayinta da aikatawa.

Kamar yadda ya faɗa, Amal Umar ta yi yunqurin ba wa wannan ɗan sanda mai suna ACP Salisu Bujama toshiyar baki, don ya rufe binciken da ake yi wa saurayinta, wanda ake zargin da sa hannunta a ciki.

Idan mai karatu zai yi waiwaya a baya, kafafen yaxa labarai da dama sun ruwaito a ranar 18 ga Agusta, 2022, cewa wani attajirin ɗan kasuwa ya shigar da koke a hannun Mataimakin Babban Sufeton ’Yan Sanda na Ƙasa, AIG Umar, da ke Shiyya ta 1, inda yake karar saurayin Jaruma Amal Umar mai suna Ramadan Inuwa, wanda ya ce, ya ba wa zunzurutun kuɗi har miliyan 40, don yin kasuwancin wayoyi, sai dai tun da saurayin nata ya karbi kuɗin ya yi vatan dabo.

A cewar CSP Bashir, sun gayyaci Jaruma Amal ne sakamakon binciken da suka yi kan lamarin, inda suka gano daga cikin kuɗaɗen da Ramadan Inuwa ya gudu da su, ya tura wa jarumar Naira Miliyan 13. Don haka ne suka gayyato ta domin amsa tambayoyi.

Ya kuma ƙara da cewa, jarumar ta amsa cewa, kuɗin na saurayinta ne, sai dai ta musanta adadinsu, inda ta ce, miliyan takwas ne ba 13 ba. Sannan bayan bayar da belin nata ne, ta nemi kotu da ta dakatar da wannan binciken da ake yi mata.

CSP Muhammad ya yi karin haske da cewa, “lokacin da ta zo na farko, ta zo da motarta, tana nan hedikwata na Zone 1. Bayan ta dawo sai ta yi yunkurin ba wa shi ɗan sanda ASP Salisu Bujama cin hanci na dubu ɗari biyar, domin a yi hakuri a kashe wannan magana kuma a ba ta motarta ta tafi da ita.” 

Daga karshe ya bayyana cewa, sun aminta da karɓar toshiyar bakin ne, don samun hujjar da za su yi amfani da ita, don maka ta a kotu, inda ya bayyana cewa, ta faɗa tarkon da suka ɗana mata, domin ta bayar da Naira 250,000 a matsayin kafin alkalami. 

Baya ga haka, CSP Bashir ya yi alwashin cigaba da binciken waɗannan kuɗaɗen da suka yi ɓatan dabo a tsakanin Jaruma Amal Umar da kuma saurayinta Ramadan Inuwa har sai sun ga abinda ya ture wa buzu naɗi.

A nata jawabin Jaruma Amal ta musanta wannan zargin da ake yi mata, inda ta wallafa a shafinta na sada zumunta na Instagram tana mai karyata zargin bayar da toshiyar baki da ‘yan sandan ke yi mata.

Jarumar ta wallafa hoton takardar umurnin kotu da ke nuna ta barranta daga zargin da ake yi mata, sannan ta yi rubutu a kasansa, kamar haka; “Kun taɓa jin mutum ya bayar da cin hanci bayan kotu ta yanke hukunci.

To jama’a, ga dalilin karan tsanar da ‘yan sanda suka sa min. Na ci nasara a case ɗin da muka yi, inda kotu ta umurce su da su fito su ba ni haƙuri, su kuma biya ni Naira miliyan ɗaya na ɓata suna. Daga nan suka sa min tarko ta yadda suma sai sun wulaƙanta ni. Toh jama’a ku ba wa kanku amsa, wannan shi ne dalili. Ina godiya masoyana da addu’o’in ku, sai wanda Allah yake so yake jarrabta.”

Babban abin tambaya a nan shine, idan har da gaske ne Amal ta bayar da cin hanci, me ya sa ’yan sanda suka hana ta motarta duk da hukuncin da kotu ta yanke har ta yi yunkurin ba su cin hanci? Wakilinmu ya nemi jin ta bakin kakakin rundunar, amma hakan ya ci tura.

Tuni dai abokan sana’arta suka shiga kafafen sadarwa su na yin kiraye-kirayen yi wa jarumar adalci.