Yanzu-yanzu: An ceto ɗaliban tsangaya da aka yi garkuwa da su a Sakkwato

Kimanin makonni biyu da suka gabata ne aka ‘yan bindiga suka sace yaran su 15 a wata makatrantar tsangaya da ke kauyen Gidan Bakuso a yankin Kaeamae Hukumar Gada.

MANHAJA ta kalato cewa, ‘yan bindigar da suka yi awon gaba da yaran sun bukaci a a biya su Naira miliyan 20 kafin su sako yaran.

Shigaban makaranar, Liman Abubakar, shi ne ya bayyana wa majiyarmu haka a ranar Talata.

Ya zuwa hada wannan labari, babu wani cikakken bayani kan ko sai da aka biya kudin fansa kafin aka sako yaran ko kuwa a’a.