Gyaran masallacin Idi: Sanata Barau zai kashe sama da Naira miliyan 400 a Bichi

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Sanatan Kano ta Arewa kuma mataimaki shugaban majalisar datttawa ta ƙasa, Barau Jibrin Maliya, ya bada umarni fara aikin zagaye babban masallaci Idi na Masarautar Bichi tare da saka interlocks.

Da yake jawabi lokacin ƙaddamar da aikin jagoran tafiyar gidan Sanata Barau I. Jibrin na ƙaramar hukumar Bichi Sani Muƙaddas Barden Bichi wanda Alh. Garba Ɗandawaki ya wakilta, ya ce Sanatan ya bada umarnin yin aikin ne saboda kishinsa ga addinin Musulunci.

Ya ce ba yi mamakin irin wannan aikin Allah da Sanata Barau Jibrin zaiyi ba, domin daman aikin sa ne ya saba a duk lokacin da buƙatar addini ta zo gabansa. Wannan masallaci za a zagaye shi asa masa Interlock da duk abinda yake buƙata domin mayar da shi na zamani.

Sanata Barau Jibril ya ce Sanatan zai kashe aƙalla sama da Naira miliyan ɗari huɗu wajen gyara masallacin irin na masarautar Bichi dake garin na Bichi.

Shi ma a nasa jawabin, kantoman ƙaramar hukumar Bichi Ahmad Kado ya yaba wa Sanata Barau Jibril da ya ɗauki gabarar gudanar da wannan gagarumin aikin a Bichi.

“Masarautar Bichi da ƙaramar hukumar Bichi sun amfana da ayyuka da dama daga Sanatan yankin Barau Jibril. Ayyukan da Barau Jibril ya gudanar babu shakka sun taimaka wajen inganta rayuwar al’umma da kuma kawo cigaba a masarautar ta Bichi.

Ya ce ƙaramar hukumar Bichi a shirye take a koda yaushe idan an kawo kavakin alheri ta ba da duk gudunmuwar da ake buƙata.

Taron dai ya samu halartar Sakatare Ƙungiyar Cigaban Masarautar Bichi Injiniya Bello Gambo Bichi da mataimakin shugaban Ƙaramar Hukumar Bichi Habibu Musa Fagolo da babban Limamin Masarautar Bichi Sheikh Lawan Abubakar da sauran manyan baƙi.