Daga BASHIR ISAH
Rundunar ’Yan Sanda a Jihar Katsina ta bayyana cewa, ta samu nasarar ganin bayan wasu ’yan fashin daji su biyar sannan ta kuɓutar da sama da mutum 100 kanata ƙwato dabbobi 658 da aka sace a jihar duk a cikin watan Maris da ya gabata.
Rundunar ta ce a cikin watan Maris ɗin da ya gabata, ta samu rahoto daban-daban har guda 51 a kan aikata manyan laifuka da suka haɗa da garkuwa da mutane, fashi da makami, satar shanu, kisan kai da dai sauransu.
Ta ƙara da cewa, ta samu tura kes 30 zuwa kotu daga adadin rahoton da ta samu na laifuffukan da aka aikata.
Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, ASP Abubakar Sadiq Aliyu, shi ne ya sanar da manema labarai hakan a ranar Juma’a a Hedikwatar rundunar, inda ya ce an kama mutum 64 da ake zargi da aikata laifuffukan.
A bayanin nasa, jami’in ya ce ana zargin 9 da aikata fashi da makami, 11 da laifin kisa, 29 da laifin fayɗe, yayin da ake zargin mutum 19 da aikata mabambanta laifuffuka.
