Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Ɗan Majalisar Dokokin Jihar Kano mai wakiltar ƙananan hukumomin Ɓagwai da Shanono, Alhaji Halilu Ibrahim Kundila ya rasu.
Majiyar Blueprint Manhaja ta nuna cewa ɗan majalisar wanda ya raba kayan agaji ga al’ummar mazaɓarsa a makon jiya, ya rasu ne a gidansa da yammacin Asabar.
An gudanar da sallar jana’izar Alhaji Halilu Ibrahim Kundila ɗan jam’iyyar APC a safiyar Lahadi a unguwar Kundila da ke ƙaramar hukumar Shanono ta jihar Kano.
Daga cikin waɗanda suka halarci sallar jana’izar akwai ɗan majalisar wakilai ta ƙasa mai wakiltar Shanono/Ɓagwai, Honarabul Yusuf Ahmad Badau da sauransu.
Marigayin mai shekaru 59, ya rasu ya bar mata huɗu da ‘ya’ya 17.
