Ranar Ma’aikata: Ƙarin albashi da kashi 35 ɓata lokaci ne — NLC

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya (NLC) ta yi watsi da ƙarin albashin da Gwamnatin Tarayya ta yi musu a matsayin “vata lokaci.”

Manhaja ta ruwaito a daren Talata cewa gwamnatin ta yi wa ma’aikatanta ƙarin kashi 25 zuwa 35 na albashinsu; ’yan fansho kuma kashi 20 zuwa kashi 28.

Sanarwar da mai magana da yawun hukumar kula da albashi ta ƙasa (NSIWC), Emmanuel Njoku, ya fitar ta duk ƙarin za su fara aiki ne daga watan Janairun 2024.

Njoku ya kuma shaida wa Manhaja cewa za a biya ma’aikatan cikon ƙarin albashin na watannin da suka gabata.

Sanarwar ƙarin ta fito ne sa’o’i kaƙan kafin Ranar Ma’aikata ta Duniya, wanda hakan ya sa ake ganin ƙarin wani albishir ne ga ma’aikatan gwamnati.

Kazalika ƙarin albashin da aka yi, yana daga cikin shawarwarin kwamitin mutum 37 daga gwamnati da ‘yan ƙwadago da sauran masu ruwa da tsaki da gwamnati ta kafa kan ƙarin albashi, karsashin jagorancin tsohon shugaban ma’aikata, Bukar Goni Aji, a watan Janairu.

Sai dai, ƙungiyar NLC ta bakin mataimakin sakatarenta, Chris Onyeka, ya ce ƙarin albashin da aka yi vata lokaci ne kawai domin hukumar ba ta da hukurmin ƙayyade mafi qarancin albashi na qasa.

“Abin da suka ce sun yi ɓata lokaci ne, ba shi da amfani a wurinmu da wurin ma’aikatan gwamnati,” in ji Onyeka a ganawarsa da wakilimu.

Sai dai duk da cewa wakilinmu na samun ƙarin bayani, jami’in na NLC ya ƙi ƙara cewa komai kan lamarin.

Mun yi ƙoƙarin samun ƙarin bayani daga wasu manyan jami’an NLC da takwarorinsu na ƙungiyar ma’aikata (TUC) amma hakan bai samu ba a daren.

NLC da sauran ƙungiyoyin ƙwadago dai na kira ne da a sanya mafi ƙarancin albashi ya zama wanda zai wadaci ma’aikaci, gwargwadon yanayin tsadar rayuwa a ƙasar.

Sun bayyana cewa idan za a sa mafi ƙarancin albashin, dole a yi la’akari da yadda farashin kayan masarufi suke tashi, musamman bayan janye tallafin mai da gwamnatin ta yi.

Ana iya tuna cewa ƙungiyar ma’aikatan jami’an sun ƙeƙashe ƙasa cewa ba za su amince da mafi ƙarancin albashin da ya gaza Naira dubu 300 a wata ba.

A lokacin shirye-shiryen Ranar Ma’aikata dai shugaban TUC na ƙasa, Festus Osifo, ya ce bangarensu na kan tattauna da kwamitin George Akume kan ƙarin albashi.

A cewarsa: “Da farko TUC ta gabatar da N447,000 a matsayin mafi qarancin albashi, amma daga bisani sun daidaita na da NLC don haka ya ƙaru zuwa N615,000.

“Game da kwamitin da ke aikin sa mafi ƙarancin albashin kuma, har yanzu bai kammala aikin ba…. da wuya a ranar 1 ga Mayu Gwamnati ta sanar da karinsa zuwa N500,000 da muke sa rai,” in ji Osifo.

Njoku ya bayyana cewa kwamitin da ya ba da shawarar, daban ne da wanda Sakataren Gwamnati, Sanata George ke jagoranta kan buƙatun ƙungiyoyin kwadago kan albashi.

Wasu manyan jami’an gwamnati dai sun bayyana cewa an sanar da ƙarin albashin ne domin guje wa abin kunya da ke iya faruwa a lokacin bikin zagayowar ranar ma’aikata.

Wani daga cikinsu ya bayyana cewa kungiyoyin ƙwadago sun yi niyyar yin amfani da ranar domin nuna wa shugabannin siyasa yatsa.

Ɗaya daga cikinsu ya ce bangaren gwamtani da jami’an tsaro ya kasa samun ganin shugabannin ƙwadago domin tattaunawa da nufin dakile yiwuwar zanga-zanga.

A cewarsa, akwai yiwuwar da gangan shugabannin ƙungiyar suka boye domin kada ɓangaren gwamnatin ya samu shawo kansu kan abin da suka shirya.

Gabanin yanzu, wata majiyar ta bayyana cewa zaman da hukumomin tsaro da ɓangaren gwamnati karkashin jagorancin Akume, suka yi da ’yan kwadagon a ranar Juma’a ya tashi ne ba tare a an cin-ma wata kwakkwarn sakamako ba.

By Editor