Daga UMAR GARBA a Katsina
Rundunar haɗin gwiwar jami’an tsaro a jihar Katsina, ta samu nasarar kuɓutar da wasu fasinjoji 17 mafi yawansu maza da ‘yan ta’adda suka sace a yankin Solar General na ƙaramar hukumar Batsari dake jihar Katsina.
A cewar wata majiyar soji, nasarar da aka samu ta biyo bayan kiran gaggawa da aka yi wa jami’an tsaron a ranar 11 ga Mayu, 2024, da misalin ƙarfe 12:00 na dare.
Saboda haka ne, rundunar sojojin Nijeriya ta 9, tare da haɗin gwiwar rundunar ‘yan sanda a Katsina, da jami’an tsaro na al’umma, da mafarauta na musamman, da mafarauta na garin Batsari, suka yi gaggawar isa wurin da lamarin ya faru don kai ɗauki.
Koda suka isa wurin, bayan musayar wuta tsakanin ɓangarorin biyu, jami’an tsaron haɗin gwiwar sun yi artabu da ‘yan ta’addan, inda daga bisani suka ci ƙarfinsu lamarin da ya tilasta ‘yan bindigar tserewa cikin wani daji dake kusa da inda lamarin ya afku, tare da barin waɗanda suka sace a nan.
An yi nasarar ceto dukkan fasinjojin da aka sace daga bisani aka miqa su ga jami’an gwamnati na ƙaramar hukumar ta Batsari, kamar yadda majiyar sojan ta bayyana.
Daraktan yaɗa labarai na gwamnan jihar Katsina, Ibrahim Kaula Muhammed ya ce, sojoji na ci gaba da aiki a yankunan jihar Katsina domin daqile ci gaba da aikata miyagun laifuka tare da tabbatar da tsaron mazauna yankin.
