Gwamna Soludo ya sauke shugabannin ƙananan hukumomi

Spread the love

Gwamnan Jihar Anambra, Chukwuma Soludo, ya sauke shugabannin ƙananan hukumomi 21 da jihar ke da su.

Haka nan, Gwamnan ya buƙaci saukakkun ciyamomin da su miƙa ragamar aiki ga shugabannin sassan gudanarwa na ƙananan hukumomin.

Bayanin haka na ƙunshe ne cikin sanarwa mai ɗauke da da hannun Kwamishinan Kula da Harkokin Ƙananan Hukumomi da Sarautun Gargajiya na Jihar, Collins Nwabunwanne, da kwanan wata 17 ga Mayu.

Ya zuwa ranar Litinin, 20 ga Mayu ake sa ran waɗanda lamarin ya shafa su miƙa ragamar aiki ga waɗanda suka dace.

A cewar wasiƙar: “Biyo bayan ƙarewar wa’adinka a matsayin shugaban kwamitin miƙa mulki, ana buƙatar ka miƙa ragamar aiki Shugaban Sashen Gudanarwa na Ƙaramar Hukuma.

“Wannan umarni ya soma aiki ne daga ranar Litinin, ga Mayu. Godiya da hidimar da aka yi wa jihar,” in ji wasiƙar.

By Editor