Daga AMINA YUSUF ALI
A tattaunawarmu da Badamasi Aliyu Abdullahi wanda aka fi sani da likitan sana’a, wanda ƙwararre ne a kan sanin madafa da mafita a game da sana’o’i da dabarun bunƙasa tattalin arziki.
Ya bayyana mana wasu hanyoyi da mai sana’a zai gane cewa sana’ar da yake ciki ko aikin da yake yi sana’a ce ko aiki ne mai kyau da ya dace da shi.
A tattaunawar ga wasu dalilai da ya kawo.
- Idan kana shauƙin ta.
Son sana’arka shi ne tubalin gina ta da yin haƙuri da juriya da kasuwanci ke buƙata. Idan ba soyayyar abinda ka ke yi a zuciyarka, ko nasara ka yi, ba za ka ji daɗin ta ba ballantana ka yi alfahari da ita.
- Idan akwai buƙatar ta.
Ita kasuwa abinda ta ke so kuma masu saye su ke buƙata shi ake kai mata, ba abinda ka ga dama ba. Buƙatar hajar mai sana’a ita ce ta ke kawo ciniki da ɗorewa.
- Idan tana tafiya da zamani.
Ko dai sana’a ta tafi da zamani ko kuma zamani ya tafi da ita (ta gushe a daina yayin ta).
- Idan bincike ya jaddada tabbacin ta.
A kowacce masana’anta ana samun alƙaluma da masu bincike, masana ko manazarta suke fitarwa. Waɗannan alqaluma ko dai su fitar da farin rubutu ko kuma baƙi a kan sana’a. Idan sun nuna fari, to a cigaba da gashi.
- Idan akwai mutane da yawa waɗanda suka samu rufin asiri da ita.
Duk sana’ar da ba ta rufa asirin masu yin ta, ba ta ka ba ce. Akwai nau’ikan sana’o’i da in ka kuskura ka shige su, to ka kulle kan ka. Ka tabbatar akwai masu yin ta da ta rufawa asiri sosai.
- Idan akwai wasu da su ka yi arziƙi sosai da ita.
Wani yana fara sana’a ne don ya samu na abinci. Wani kuma don ya samu rufin asiri. Wani kuma arziƙi ya ke da burin yi. Kowa da irin nasa burin. Ko wane irin buri ne da kai, idan ka ga akwai masu arziƙi a irin sana’ar da kake, alama ce ta cewa rami ne mai ɓullewa.
