Hajji: Aƙalla mahajjata 900 ne suka rasu saboda tsananin zafi

Spread the love

A cewar jaridar AFP, aƙalla mahajjata 600 daga ƙasar Misra suka rasu. Yayin da suke kai adadin a jumlace zuwa 922 a wata ƙididdiga.

An sami yawaitar zuwa asibitoci a lokacin aikin hajji, yayin da cigiyar wanda suka ɓace shima ya yawaita. Duk da wannan rahoton na cewa mahajjata 900 suka rasu lokacin aikin hajji, shugaban hukumar alhazai ta ƙasa yace yan najeriya uku ne ƙadai suka rasu.

Ya ƙara da cewa, aƙalla mutum 17 ne suka suma saboda tsananin zafi, amma kawo yanzu duk an basu kulawa sun dawo hayyacinsu. An ƙara samun mata biyu masu ciki wanda sukai ɓari, da kuma mutum biyar masu ciwon zuciya.

Duk wannan an sameshi ne saboda an shirya ma aikin hajjin sosai daga ɓangaren hukuma. Ya ƙara da cewa da an gama mayar da alhazai gida Najeriya, shirye-shirye zai fara na aikin hajjin 2025.

By ukarofi