Daga DAUDA USMAN a Legas
Shugaban Ƙungiyar Izala ta Ƙasa, reshan Jihar Legas Shiekh Suleman Ibirahim kuma babban limamin masallacin Juma’a na rukunin gidajen unguwar Wantauzan a Legas, ya shawarci maniyyatan Nijeriya masu zuwa ƙasa mai tsarki domin sauke faralin su a wannan shekara da su ji tsoron Allah.
Ya ce, su guji sayen haramtattun kayan da Gwamnatin ƙasar Saudiyya ta haramta a shigar mata da su a ƙasar ta bakiɗaya.
Babban limamin na masallacin ya buƙaci hakan ne a lokacin da yake gabatar da huɗubar sa ta sallar Juma’a ga al ummar Musulmin Nijeriya a ranar Juma’ar makon da ya gabata.
Huɗubar tasa ya taɓo wuraren da suka shafi yadda ake gudanar da ayyukan aikin Hajji.
Ya cigaba da jawo hankulan maniyatan na Nijeriya masu zuwa ƙasa mai tsarki domin sauke faralin su a wannan shekara da su ƙara ƙoƙari a wajen gudanar da ayyukan hajjin su bisa ƙa’ida kamar yadda addinin Musulunci ya ummurci Musulmi su yi a lokacin da suke gudanar da ayyukan aikin hajji.
Babban limamin ya ce, kuma yin aikin hajji tare da bin ƙa’idojin aikin hajji, ya samu hajji kar babbiya a wajen ubangiji wato ya samu hajji mabaruru haka.
Hakazalika, ya cigaba da cewa, kuma har idan aikin hajji ya samu yin aikin hajji kar babbe a wajan ubangiji to kuma Allah ubangiji ya shafe masa zunuban sa gabaɗaya wanda ya ɗauka tun lokacin yana yaro zowa wannan lokaci yace tun daga lokacin da aka yi ƙaramar salla zowa yanzu wa’azin da suke yi na sati bibiyu a waɗansu unguwanin jihar Legas.
Ya ce, suna yin sune a bisa kan ayyukan aikin hajjin wannan shekare, akan haka yake ganin ya kamata ya bai wa maniyyata masu zuwa ƙasa mai tsarki a Nijeriya domin sauke farali a wannan shekara dama masu ra’ayin zuwa a shekerun gaba masu zuwa da su cigaba da yin karatu tare da neman sanin yadda ake gudanar da ayyukan aikin hajji da sauran makamantan su.
Ya ƙara da ceaa, da fatan maniyyatan na Nijeriya da sauran masu ra’ayin zuwa ƙasa mai tsarki domin sauke faralin za su ɗauki wannan shawara tashi.
A ƙarshe ya ce, yana yi wa dukkan al’umma fatan alheri a wajan gudanar da shagulgulan babbar sallah lafiya.
