“Kar ka sauke Sarkin Musulmi”- MURIC ta gargaɗi Gwamnan Sakkwato

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Ƙungiyar kare ƴancin al’ummar musulmin Najeriya (MURIC), ta gargaɗi gwamnan Jihar Sakkwato, Aliyu Ahmad cewa kar ya sauke Sarkin Musulmi, Sultan Sa’ad Abubakar, daga kan muƙaminsa.

MURIC ta yi wannan gargaɗi ne biyo bayan da gwamnan ya sauke sarakunan gargajiya guda 15 a faɗin Jihar watanni biyu da suka wuce inda jita-jitar sauke Sarkin Musulmin ke yawo wanda hakan ya sa ƙungiyar ta nuna damuwa tare da kira ga gwamnan da ya guji duk wani yunƙuri na sauke Sarkin Musulmi daga kujerarsa.

Daraktan ƙungiyar, Farfesa Ishaq Akintola ya faɗi hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, inda ya ce duk da cewa gwamnan ya sauke sarakunan gargajiya 15, bai dace ya kuma tunkari Masarautar Sultan Sa’ad ba domin kujerar ba ta gargajiya ba ce, ta dukkan Musulmi Najeriya ce, don haka ya ke shawartar gwamnan da ya kiyaye daga batun sauke Sarkin.

Farfesan, ya kuma yi kira ga majalisar dokokin Jihar, da su yi kokarin gyara dokar dake cewa gwamna na iya sauke dukkan sarakunan gargajiya ciki har da Sarkin Musulmi ta yadda ba zai samu ikon haka ba ga Sarkin Musulmi.

By Babaji