Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Gamayyar ƙungiyoyin farar hula na yankin Arewacin Nijeriya, CNG, sun jaddada cewa kotu ce kawai ke da hurumin yanke hukunci kan makomar jagoran haramtacciyar ƙungiyar Biyafara ta IPOB a yankin kudu maso gabashin ƙasar, Nnamdi Kanu ba Gwamnatin Tarayya ba.
Wannan martani ya biyo bayan ƙoƙarin da wasu gwamnoni da ‘yan majalisar dokokin tarayya na shiyyar kudu maso gabashin Nijeriya, wato yankin al’ummar Ibo ke yi na neman gwamnatin Nijeriya ta saki jagoran na IPOB, duk da kasancewar yana fuskantar shari’a a gaban kotu, bisa zarge-zargen aikata laifuka da suka shafi cin amanar ƙasa.
Shugaban CNG, Jamilu Aliyu Charanchi ya bayyana, “kowa na sane da yadda aka halaka mutane tare da ƙona dukiyoyin miliyoyin nairori na mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba, wanda kuma kowa ya san cewa Nnamdi Kanu da muatanensa ke aikatawa”
“Duk wanda ya san abun da yake yi, kuma ya ke son ci gaban ƙasarsa, ba za ka same shi yana maganar sakin Kanu ba, a daidai lokacin da har yanzu mutanensa na cigaba da miyagun ayyuka, wannan cin mutunci ne ga gwamantin Bola Tinubu, da ita kanta APC, ” inji shi.
Ya ƙara da cewa, “Har yanzu mutumin nan bai taɓa fitowa ya nemi yafiyar iyalan sojojin da ya kashe, da masu dukiyoyin da ya ɓarnatar mu su haƙƙinsu ba, kuma har yau ’yan uwansa na cigaba da kashe jama’a”.
Shuhugaban ya ce, “yanzu ta tabbata kenan zargin da mutane ke yi cewa ba Nnamdi Kanu ne kaɗai ke aikata irin waɗannan laifuka, da goyon bayan shugabanin yankin da ya fito, tun da babu yadda za a yi ka ce za ka nemi a saki mutumin da ka san yana aikata laifi, in ba don kana goyan bayansa ba.”
Shugaban gamayyar ƙungiyoyin ya cigaba da cewa, laifin da ake zarign Nnamdi Kanu da aikatawa na samar da dakarun sojojin a yankinsu har su ayyana ficewa daga Nijeriya laifuka ne na cin amanar ƙasa ba wai gwagwarmaya ba.
