Gwamnatin Tarayya ta soke biyan haraji kan shinkafa,alkama da masara da aka shigo daga waje

Spread the love

Gwamnatin Tarayya ta sanar da dakatar da haraji akan wasu nau’in abinci.

Ministan Noma, Abubakar Kyari, ya bayyana wannan a lokacin taron manema labarai a cibiyar watsa labarai na Ƙasa, Abuja a ranar Litinin.

Kyari ya bayyana cewa abincin sun haɗa da masara, alkama, shinkafa da wake. Gwamnati ta bada damar shigo da su ba tare da biyan haraji ba na tsawon kwanaki 150.

Ya ƙara da cewa wannan mataki yana cikin Shirin gaggawa na Shugaban Ƙasa ya ɗauka domin rage hauhawar farashi da ke damun ƙasar.

Ministan ya ce gwamnati ta na aiki tuƙuru don magance matsalar ƙaruwar farashin abinci, wanda ya sa farashi ya yi ƙaruwar da ba a taɓa gani ba.

By ukarofi