MAKAMASHI: Babu inda ’yan tasha za su kai mu sai halaka

Spread the love

Tare da BASHIR MUDI YAKASAI

Najeriya da farkon fari, arzikin wannan ƙasa, musamman ma arewacin wannan ƙasa shine noman abinci da suka haɗa da dawa da gero da maiwa da rogo da makani (walihan) da doya, sannu a hankali alkama da sha’ir da shinkafa ’yar Hausa suka kankama suka zama ’yan gida duk da cewa farin wake da jan wake su na yi mu su dabaibayi. Sai da ta kai gidan kowa a duk kaka sai ka tarar da runbuna cike makil da abinci, babu abin da yake biyo baya illa bukukuwa na samari da ’yan mata da zawarawa har ma da na sakin wawa na wannan shekarar.

Zuwan Turawan mulkin mallaka sun zo da wata tsirfa na noman da suka kira “cash crops”, wanda ya haɗa da gyaɗa, da auduga da kashu da riɗi a yankin Kudu suka sa su noman kwakwar manja da roba haka tilasa ma na noman rake.

Haka a kiwon dabbobi kamar shanu da tumaki da awaki da tsintsaye kamar kaji da zabi da agwagi da kuma ana kiwon su ne domin a matsayin kadara ko kuma domin biyan buƙata a lokacin bukukuwa na al’ada da kuma domin biyan buƙata a lokacin bukukuwa na al’ada da kuma addini kamar lokacin layya a lokacin bikin babbar sallah. Zuwan Turawa suka cusa ra’ayin “Kiwo Don Riba”, domin su sami fatu da ƙiraga.

Da mulkin jama’a ya koma hannun ’yan tasha da mata ’yan gudun casa da sussuka da surfe, waɗanda ake kira a taƙaice ’yan gudun niƙa. Haka ’yan tasha yawancinsu, ’yan gudun noma ne na abinci ko na kuɗi, bayan kuma ’yan mulkin mallaka sun sharɗanta da shi za a biya haraji saboda haka dole a gudu, kuma babu gurin zuwa illah tashar jirgin ƙasa ko kuma tashar mota.

Su ne su ka haɗu da ’yan takarda wato “Eh” waɗanda yanzu suka rikiɗe suka zama ɓarayin biro, inda su ke sata ta rashin kunya kamar ɓerayen tanka, wato sata rana tsaka babu tsoran duk wani mahaluki.

Ta kai ta kawo, ɓarawon biro a wannnan ƙasa shine zai ƙarar dan sanda ko kuma duk wani jami’in tsaro da kada ya kuskura ya taɓa shi ko iyalinsa ko dukkan wanda yake mu’amala da shi kan sata da ake tuhumar sa da ita. Ta kai ɓarawon biro shi ne sarkin gari kuma sarautar mai darajar sarkin yanka. Ana ji ana gani ’yan tasha su ne waziran shugaban, malaman addini su ne su ka zama bokaye da ’yan tsubbu da kuma ’yan damfara.

Ba ka neman wata shaida, je ka gidan malaman kai ka ce, ’ya’ya da jikokin agalawa ’yan kiri, wato ’yan kasuwar Kano ko Katsina ko Daura ko kuma Zazzau. Tun daga 1999 da mulki ya bar hannun sojoji da ’yan sanda ya dawo hannun ’yan giri, wato “NOAƊING” banda cuta da yaudara da kuma zambata, wannan shi ya haifar da hahhawar farashi da tsadar rayuwa. Mulkin ‘yan tasha yayi nuni da cewa basu da imani ko na ƙwayar zarra.

Misali a watanni ukun farko na wannan shekarar ta 2024, jihohi 30 daga cikin 36 sun kasha naira na gugan naira Biliyan 960 a wajen sayen kayan ƙwalam da maƙulashe yayin taruka da tafiye-tafiye tare da iyalinsu da kuma ‘yan rakiya. An tattaro wannan bayani ne na kece raini ne da dukiyar talakawan ƙasannan ta hanyar amfani da bayanan da shafin Budget da ke wallafawa wanda ke dauke da bayanan kuɗin da gwamnatoci ke kashewa a jihohinsu. Inda jihata ta Kano ta kasha Biliyan Talatin da Hudu da Miliyan Arba’in da ɗaya (N34.41B). Yanzu kana tuhuma sai ace kai dan hamayya ne. Shima shugaban ƙasa Tinubu da mataimakin sa Shettima sun kasha naira Biliyan 8 da Miliyan ɗari 6 wajen tafiye-tafiye cikin watanni uku.

Mun dauko wannan dogon bayani ne domin ku masu karatu ku fahimci cewa Najeriya ta faɗa hannun ‘yan tasha masu “cin ƙwala da Bado” a kasannan tun zuwan mulkin damokaraɗiyya a shekara ta 1999 a cikin waɗanda suke mulkin “wannen kare ne ba bare ba” batare da tsoro ba bari mu kira waɗannan bara gurbin al’umma da sunan da mamallakin kamfanin na matatar man fetur mallakar Aliko Dangote yake cewa, ‘yan “Mafiya” suna yunƙurin yin zagon ƙasa a aikin matatar man daya kai Dala Biliyan 19 a Legas.

A yayin da yake jawabi a taron shekara-shekara na Afreɗim bank. Aliko Dangote yace “ ƙungiyar “Mafia” masu safarar mai sunafi ƙarfin masu safarar miyagun ƙwayoyi, waɗanda sune neman rife masa masana’anta. To, nasan cewa akwai fitina. Amma bansan cewa akwai fitina. Amma bansan cewa mafiyan man fetur sunfi ƙarfin mafiyan ƙwayoyi ba. Na tabbatar da haka”, inji shi.

Na tabbatar da haka, inji shi. Dangote, wanda ya bayyana kansa a matsayin wanda kare kansa, yace “yan mafiya sune sukayi yunƙuri daban-daban domin kare kansa da dukiyarsa. Aliko yace shi mutum ne mai kare kansa ta kowanne hali. Aliko Dangote mutum ne mai ƙwatarwa kansa ‘yanci a duk rayuwarsa. Kuma a kullum a shirye yake ya kare kansa da dukiyar sa da kuma mutuncinsa baya tsoron duk wani mafiya ɗan kwaya.

Wani albashir da Dangote yayi wa al’ummar ƙasar nan shine shirye-shiryen da yake yin a karkata hankalinsa a kasuwancin ƙarafa, wato ma’adanai. Aliko Dangote yayi nuni da cewa ƙarafa suma dukiya ce da duniya take buƙata don haka a shirye yake domin faɗawa cikin ta. Wannan hali na Dangote mu ke kira da ‘yan Najeriya su fito su shiga wannan sana’a ka da Ɓarayin zaune su tsorata su daga waje, Turai ko Amurka ko kuma ƙasashen Asia.

Idan ana son Najeriya taci gaba ta kowanne fanni sai ta sauka daga tsoron mafiyan duniya daga ko’ina suke a wannan sarari na subuhana. Kuma ‘yan ƙasa sai sun daina zaɓan yan tasha. Babu inda ɗan tasha zai kai mu illah yunwa da fatara da talauci da ƙazanta inda cututtuka zasu ta halakamu, bayan muna da makamashin man fetur da gas da kwal da rana da iska da suke jujjurawa a cikin ƙasa duk shekara, ga kuma ma’adanai da duniya ke buƙata. Wanda wasu ‘yan ƙalilan daga waje suke kwasa a jihohin Borno da Adamawa da Taraba da Zamfara da Katsina da Kaduna da Sokoto da Naija da kuma Nassarawa. Saura da me shugabanni su ce bamu yarda ba.

By ukarofi