Da ƊUMI-ƊUMI: Ƙungiyar lauyoyi ta ce babu maganar amince wa auren jinsi a Yarjejeniyar Samoa

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Ƙungiyar lauyoyin Nijeriya (NBA), ta ƙaryata rahotannin da ke cewa Nijeriya ta rattaɓa hannu kan ciyo bashin Dala biliyan 150 wanda ya ƙunshi amince wa tare da halasta auren jinsi a ƙasar.

Wata takarda da ke ɗauke da sanya hannun shugaban ƙungiyar, Yakubu Maikyau, ta ce ba a samu daidaito tsakanin yarjejeniyar da dokokin Nijeriya ba wanda akwai batun haramcin auren jinsi a cikin kundi na 2023.

Maikyau, ya ce ƙungiyar da ta shawarci Nijeriya kan sanya hannun matuƙar akwai dokar da ta ci karo da dokokin Nijeriya.

Ya kuma yi kira ga gwamnati da ta cigaba da wayar da kan al’umma a kan yarjejeniyar tare da kira ga masu-ruwa-da-tsaki da su ilimantar da mutane kan haƙiƙanin abin da yarjejeniyar ta ƙunsa.

Kazalika ya ce za su cigaba da aiki da gwamnati ta hanyar ba ta shawarwari da kuma tabbatar da adalci ga al’ummar Nijeriya baki ɗaya.

By Babaji