Shugaban Jami’ar Tarayya ta Dutsinma (FUDMA), Jihar Katsina, Farfesa Armaya’u Bichi, ya zargi cewa wasu daga cikin ma’aikatan jami’ar suna aiki a matsayin masu bayar da bayanai ga ‘yan bindiga.
Ya bayyana cewa ‘yan bindiga sun yi ta kai hari a yankin, suna sace dalibai da ma’aikata na jami’ar da kuma ‘yan’uwansu.
Kwana bakwai da suka wuce, ‘yan bindiga sun kai hari gidan Dr Tiri Gyan David, Shugaban Sashen Tattalin Arzikin Noma, faɗaɗa da bunkasar Karkara na jami’ar, suka kashe shi kuma suka sace ‘ya’yansa.
A ranar Talata, yayin wata ganawa da ‘yan jarida, Bichi ya ce an ba da lambobin wayar wasu ma’aikatan da ake zargin ga hukumar tsaro don ci gaba da bincike.
Bisa ga cewar shugabancin makarantar sunayin duk abin da za su iya yi don hana maimaita irin wannan lamari amma yanayin ya kara muni.
