Tsohon ɗan wasan gaba na Liverpool, Firmino ya zama fasto

Spread the love

Tsohon ɗan wasan Liverpool Roberto Firmino ya sanar cewa ya zama limamin coci.Ɗan wasan na Brazil ya bayyana hakan ne a shafukansa na sada zumunta, inda ya bayyana wannan lamarin a mastayin gagarumin sauyi a rayuwarsa.

Firmino, tare da matarsa, sun zama Fasto a cocin da suka kafa shekaru uku da suka wuce. An gudanar da bikin sadaukarwar ne a ranar Lahadin da ta gabata a garinsu na Maceio.

A cikin saƙo mai ratsa zuciya, Firmino ya bayyana cewa zama fasto abu da ya sameshi bayan nazari mai zurfi cikin lamarin Yesu.

“Tun lokacin da na fara nazari akan Yesu, sha’awar zama cikin masu yi mai hidima ya narke a zukatanmu.

Ya kuma mika godiyarsa ga fastoci Jairo da Keila don ƙarfafa masa gwiwa a cikin wannan tafiyar ta ruhi.

Firmino ya yi rawar gani a Liverpool daga 2015 zuwa 2023, inda ya samu manyan kofuna bakwai, ciki har da gasar Premier ta 2019/20 da gasar zakarun Turai ta 2018/19.

Ɗaya daga cikin fitattun lokutansa shine ya zura ƙwallo mai mahimmanci a wasan karshe na cin kofin kulobna duniya a 2019, inda ya tabbatar da nasarar su.

A kakar wasan data gabata Firmino ya buga wa kungiyar Al-Ahli wasanni 34 inda ya zura kwallaye tara. Ya kuma wakilci tawagar ƙasar Brazil, inda ya halarci gasar cin kofin duniya ta 2018.

A halin yanzu, Roberto Firmino ya ci gaba da taka leda a kulob din Al-Ahli na kasar Saudiyya, inda ya buga wasanni 34 a dukkan gasa a kakar da ta wuce, inda ya zura kwallaye tara sannan ya taimaka aka zura kwallaye bakwai.

By ukarofi