Tinubu da shugabannin ƙwadago na ganawa a Fadar Shugaban Ƙasa

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Shugabannin ƙwadago sun hallara a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, domin tattaunawa na musamman da shugaba Bola Ahmed Tinubu kan batun mafi ƙarancin albashi.

NLC da TUC sun tura wakilai domin ganawa da Tinubu inda suka isa da misalin ƙarfe 2 na rana a wata farar mota ƙira bas.

Rahotanni sun ce, a tattaunawar za ta mayar da hankali ne kan batun ƙarancin albashin wanda aka ɗauki tsawon lokaci ana neman matsaya a kai tsakanin ƙungiyar ƙwadago da kuma gwamnatin tarayya.

Sakamakon zaman ana fatan ya zama ya yi tasiri ga tafiyar da harkokin Nijeriya da ma tattalin arziƙinta baki ɗaya.

By Babaji