Biyan ‘yan kwangila akan lokaci yana bunƙasa tattalin arzikin jihar Kano – Engr. Khalil

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano

An yi amanna cewa biyan ƴan kwangila akan lokaci yana inganta tattalin arzikin jihar Kano.

Manajan Daraktan Kamfanin Gerawa Global, Engr. Abubakar Ibrahim Khalil ne ya bayyana hakan a lokacin da gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya kaddamar da titin kilomita biyar da aka gina a Gwarzo, wanda gwamnatin baya ta yi watsi da shi.

Engr Abubakar Khalil ya kara da cewa, bayar da kwangiloli ga kamfanoni na cikin gida na rage rashin aikin yi a tsakanin matasan Kano da sauran al’umma,

Kazalika ya yabawa Gwamnan Jihar Kano bisa yadda ya ke baiwa ƴan kwangila ƴan asalin Kano kulawa ta musamman.

Daga karshe dai ya yi kira ga ƴan kwangilar Kano da su ci gaba da yin ayyuka masu inganci domin gwamnatin jihar Kano za ta ci gaba da ba su kwangiloli.

Blueprint Manhaja ta ruwaito manajan Daraktan Kamfanin gine-gine na Gerawa Global Construction Alh. Abubakar Ibrahim Khalil ya sha alwashin ci gaba da gudanar da ayyuka masu inganci ba a Kano kadai ba har ma a Nijeriya baki daya.

By ukarofi