
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Shugaban majalisar dattijai, Godswill Akpabio ya faɗa wa Sanatar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan cewa zauren majalisar ba kulob ba ne, don haka sai an gabatar da ita kafin ta yi magana a zaman majalisar.
Hakan ya faru ne a lokacin da majalisar ke tafka muhawara game da ƙudirin ƙirƙirar dokar majalisar sufurin motoci da dangoginsu wanda Sanatan Kwara ta Kudu, Oyelola Ashiru na jam’iyyar APC ya ɗauki nauyinsa.
Ƙudirin mai suna ‘National Road Transportation Council (Establishment) bill, 2024’ ya ƙunshi kula da harkokin sufurin da aikin yin sufurin da abubuwan da suka shafe su a Nijeriya.
Yayin da sanatoci da dama su ka goyi bayan sa, a gare guda kuma wasu da dama ciki har da Victor Umeh da Adams Oshiomhole sun ƙi amincewa da shi.
Waɗanda su ka ƙi amincewa da shi sun kafa hujja da cewa samar da majalisar zai zama maimaici ga irin ayyukan hukumar kiyaye haɗurra (FRSC) da kuma ofishin sa-ido ga motoci (VIO). Don haka, su ke neman a yi watsi da shi kasancewar gwamnati na ƙoƙari wajen tabbatar da rahoton Orosanye na haɗe wasu hukumomin da ke aiki iri ɗaya waje guda.
Sanata Natasha wacce ta bada gudunmawa a batun ƙudirin, a karo na biyu, ta sake miƙewa ba tare da umarni shugaban majalisar ba inda ta ce akwai buƙatar a yi nazari game da lamarin sufurin ruwa domin sauƙaƙe cinkoso a hanyoyi.
Ganin haka ne ya sa Akpabio ya ce “Mai girma Sanata Natasha, a majalisa sai an gabatar da ke kafin ki yi magana. Ba a kulob mu ke ba.” Yayin da ta amsa da cewa, “..a gafarce Ni.”
