Daga MAHAMMAU MUJJITABA a Kano
Kwamishinan Kula da Al’amuran Addinai na Jihar Kano, Sheikh Tijjani Auwalu ya bayyana cewa a daidai wannan lokacin da muka shiga sabuwar shekarar Musulunci ta 1446, Jihar Kano ba za ta lamunce da baɗala ba da sunan auren jinsi kamar yadda ake ta cece-kuce kan yarjejeniyar Samoa da ake zargin a cikinta akwai wasu sharuɗɗa da suka saɓa wa addinin Musulunci da kuma kyawawan al’adu.
Sheikh Tijjani Auwal ya yi wannan bayani ne a lokacin da yake hira da ‘yan jaridu a Kano Alhamis ɗin makon jiya.
“Mu a nan ma’aikatar kula da addini muna tabbatarwa da duniya cewa ma su ssumoga da fasa ƙauri ko hikimar shigo da wannan aƙida a Kano to basu da mafaka ko gurin zama a Jihar Kano mai Musulmi kashi 66 cikin 100 a wannan jiha mai albarka ta Musulinci,” inji Kwamishinan.
Haka kuma ya ƙara da cewa yadda gwamna ya ji labarin cewa akwai wasu ƙungiyoyi masu wannan aƙida a ɓoye hankalinsa ya tashi kuma ya nuna damuwarsa, don haka ne ya umarci ɗaya daga cikin hukumomi da ke ƙarƙashin ma’aikatar addini ta Kano wato HISBAH ta ta shi tsaye wajen zaƙulo ƙungiyoyi da su ke da wannan a ƙida da yaɗa ta ta hanyar dabaru da sunan ba da tallafi, wannan abu ne da wannan ma’aikata ta addini ba za ta yadda ba, kuma ta tashi tsaye haiƙan wajen ganin an kawar da waɗannan ƙungiyoyi a Kano, wanda idan ‘yan Kano ne za a hukunta su na, idan kuma baƙi ne to su gaggauta barin Kano domin ba su da makafa a jihar, domin Jihar Kano ko dukiyar duniya za a bata don ta amince da wannan aƙida, ba za ta taɓa amincewa da wannan aƙidar ba,” a cewar kwamishinan addini Hon. Sheikh Sani Auwalu.
Haka zalika ya ce dangane da sabuwar shekarar Musulunci kuwa yanzu haka an kammala kalandar Musulunci da ake bugawa duk shekara da hukumar shari’a da ke kula da al’amarin, kuma akwai tsare tsare na gabata da taro da jawabi domin wayar da kan al’umma kan muhimmancin shigowar sabuwar shekara da kuma aiki da kwanaki da watannin Musulinci wanda akan su Allah ya ɗora ibadun da muke yi na aikin Hajji, Azumi, Zakka, da sauransu duk ana la’akari ne da watannin Musulinci 12 wajen aikata waɗannan ibadu a cikin su da sauransu.
A ƙarshe Hon. Sheikh Tijjani Sani Auwalu ya yaba wa Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf kan irin gaggarumar gudunmawa da ya bai wa hukumar Alhazai da Alhazan Kano wanda haka ya kawo a zamanin gwamnatin nan ta Kano, aka yi aikin Hajji da samun gaggarumar nasara a wannan aiki na Hajji.
Haka kuma ya yaba wa gwamnan Kano kan irin tallafi da ya ke bai wa mata na Naira 50,000 duk wata wanda a wannan watan ne aka yi karo na biyu wanda mata sama da dubu 10 ne, su ka amfana da talafin dubu 50 daga ƙananan hukumomin Kano, kuma za a cigaba da wannan aikin na tallafawa mata duk wata har tsawon shekara takwas da ikon Allah ga kuma aikin bunƙasa, ilimi, lafiya, noma, sama da aikin yi ga matasa maza da mata, biyan ‘yan fansho haƙƙin su da sauran abubuwa na bunƙasa tattalin arzikin Kano da sauran al’umma baki ɗaya.
