Daga JOHN D. WADA a Lafiya
Wani babban ɗan kasuwa mazaunin birnin Lafiya fadar gwamnatin jihar Nasarawa dake harkar saye da sayar da kayayyakin noma da suka haɗa da shinkafa da masara da wake da dai sauransu, wato Alhaji Shuaibu Yusuf, ya buƙaci gwamnatoci a duka matakai musamman na jihar Nasarawa su riƙa tuntuɓar manyan ‘yan kasuwa ire-iren sa a wannan lokaci da ake cigaba da fama da matsalar tsadar rayuwa a jihar da ma ƙasa bakiɗaya don bada nasu gudunmawa.
Alhaji Shuaibu Yusuf ya bayyana haka ne a lokacin da yake tattaunawa da ‘yan jarida a ofishinsa dake bayan bankin Zenith dake Lafiya ranar Laraba 17 ga watan Yulin shekarar 2024 da ake ciki.
Ya ce ba shakka idan gwamnati tana son rage ko magance wannan matsalar ta tsadar rayuwan dole ne ta riƙa tuntuɓar ire-irensa manyan ‘yan kasuwa a jihar da ma ƙasa baki ɗaya don neman shawarwari da gudunmawar su a wannan fannin kasancewa su ‘yan kasuwan musamman shi kansa ya ɗauke sama da shekaru da dama yana harkar kayayyakin abincin na gona da hakan ya ba shi ƙwarewa da yadda zai iya bada mahimman shawarwari da gudunmawa wa ƙoƙarin gwamnatin wajen shawo kan ƙuncin rayuwar da yardar Allah.
Ɗan kasuwan Alhaji Shuaibu Yusuf wanda a yanzu haka al’ummar garin Lafiya da kewayen ta dama jihar baki ɗaya musamman talakawa suna cigaba da yaba masa dangane da kimantawa da tsoron Allah da yake nunawa a sana’ar tasa musamman na rage farashin kayayyakin abincin gonan da yake sayar musu da sauƙi sosai, ya ce ba shakka ya yanke shawarar cigaba da sauƙaƙe farashin kayayyakin nasa ne don agaza wa al’umma musamman talakawa marasa galihu cikin al’umma dake cigaba da wahala sakamakon haurawar farashin kayayyakin a ƙasa baki ɗaya a yanzu.
Har ila yau babban ɗan kasuwan Alhaji Shuaibu Yusuf ya kuma yi amfani da damar inda ya yi kira na musamman ga sauran manyan ‘yan kasuwa ire-irensa a jihar dama ƙasa baki ɗaya su riƙa bada gudunmawar su suma wajen tabbatar ana cigaba da taimakawa talakan ƙasar nan musamman ta kimantawa a yayin da suke sayar da kayayyakin nasu kasancewar a cewar sa duk wani riba da mutum ya samu wata rana zai bar su ko ya tsufa ko kuma ya bar duniyar kwata-kwata.
Wakilin mu dai ya gano cewa a yanzu haka al’ummar birnin Lafiya da kewayen ta baki ɗaya dama jihar musamman talakawa marasa ƙarfi da zarar suka samu labarin ana sauke kayayyakin abincin gonar waɗanda Alhaji Yusuf ke sayarwar cikin garaɓasar musamman shinkafa da sauran hatsin sukan yi cincirindo ne a shagon sa don sayen kayayyakin cikin farashi mai rahusa sosai fiye da yadda ake sayarwa a kasuwanni inda hakan ya sa Alhaji Yusuf ɗin ya yi suna sosai gun su kuma suna cigaba da yaba masa kullum tare da masa addu’a da fatar alheri.
